Kotu ta tabbatar da Uba Sani a matsayin ɗan takarar gwamnan APC a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kaduna ta tabbatar da Uba Sani a matsayin wanda zai tsaya takarar gwamnan Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Wani ɗan takarar gwamna, Sani Sha’aban ya garzaya kotu yana neman a soke Uba Sani a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar APC bisa zarginsa da tafka maguɗi a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a watan Mayun 2022.

A zaɓen dai an bayyana Uba Sani ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen inda ya samu ƙuri’u 1,149. Sha’aban da wani ɗan takara Bashir Abubakar sun samu ƙuri’u 10 da 37 bi da bi.

A ƙarar da Sha’aban ya shigar, an haɗe APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a matsayin wanda ake ƙara na 1 da kuma na 3 da ake ƙara.

Ya ce, jam’iyyar ta yi zargin maguɗin zaɓen fidda gwani ta hanyar sauya jerin sunayen wakilai daga unguwanni da ƙananan hukumomi da ’yan uwa da abokan hulɗarsu domin fifita wani ɗan takara.

Ya kuma ce babu wani taron wakilai a jihar, inda ya ce an yi maguɗin zaɓe.

Sai dai da ya ke yanke hukuncin a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba, 2022, Mai shari’a Mohammed Garba Umar ya yi fatali da shari’ar da ta saɓa wa tanadin manufofin Majalisar Shari’a ta ƙasa.

By Editor