Paul Biya: shugaban ƙasa mafi tsufa zai cika shekaru 40 da hawa mulki

Spread the love

Daga WAKILINMU

A ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamb, 2022, Shugaba Biya mai shekaru 89 da haihuwa, kuma mafi tsufa a shuwagabannin duniya zai cika shekaru 40 a matsayin shugaban Ƙasar Kamaru.

Kamar yadda Jam’iyyar RDPC ta sanar, zata shirya babban biki don nuna farin cikinta ga wannan rana ta cika shakaru 40 akan shugabancin Ƙasar Kamaru da shugaban jam’iyyar ya yi, wato Paul Biya wanda ya zama uba da ya asassa wannan jam’iyya ta RDPC a shekara ta 1985.

A cewar Herve Emmanuel Nkom, ɗaya daga cikin mambobin jam’iyyar, bikin zai kasance na murnar nasarorin da aka samu tsayin shekaru 40 da jam’iyyar ta yi tana mulkin ƙasar, kama daga ɗaurewar demokraɗiyya da kuma cigaba da aka samu ta ɓangaren zaman lafiya.

A yanzu haka a shalkwatar jam’iyyar da ke Messa, da yawa daga cikin mambobin jam’iyyar na kaiwa da komowa tare da cinikayyar huluna da kuma riguna masu ɗauke da hoton Shugaba Paul Bila, a ƙoƙarin su na shirin bikin na gobe.

“Mutane da dama sun zo kallon wannan gangamin na siyar da riguna da kuma huluna masu ɗauke da Shugaba Bila, kuma da yawa sun buƙaci siyan nasu,” inji Sylvie Beyala, mamba na jami’yyar.

Taron na gobe, wanda za a gudanar a Yaounde babban birnin Ƙasar Kamaru, ya samu tabbaci daga manya da kuma masu faɗa aji na ƙasar, sai dai har zuwa yanzu babu wani tabbacin uban taron zai samu halarta, wato shugaba Biya.

Paul Biya ya hau karagar mulki a ranar shida ga watan Nuwamba, shekara ta 1982 bayan ya kwashe shekaru bakwai a matsayin Firaministan.

Ya kasance shugaban ƙasa na biyu tun bayan da Kamaru ta samu ‘yancinta a shekara ta 1960.

Bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth ta Biyu mai shekaru 96, Paul Biya ya ɗare kujerar shugaba mafi shekaru a duniya.

Rigingimun siyasa da zamantakewa ta rashin tsaro na daga cikin matsalolin da suka yi wa mulkinsa dabaibayi, inda matsalar tattalin arziki ke jagorantar matsalolin.

Da haka ne wasu da dama musamman a jam’iyyun adawa suke ganin rashin cancantar sa da kuma gazawar sa a shugabantar ƙasar, a cewar su, shekarunsa kawai za su iya kawo tasgaro ga cigaban da ake fatan samu a ƙasar.

Wannan dalilin ne ya sa da yawa daga cikin jam’iyyun adawa da kuma ‘yan ra’ayi irin na su suka yi kira ga al’ummar Ƙasar Kamaru da su zauna gidajensu a gobe, kada su fito wannan biki da ake shirin gudanarwa, a cewar su babu wani abin tunawa na farin ciki dangane da mulkin shugaba Paul Bila.

By Editor