Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mahara sun ƙone wata Kotun Majistare a Owerri, babban birnin Jihar Imo, ƙasa da sa’a 24 da aka kai makamancinsa a wata babbar kotun jihar da ke yankin Orlu.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne ta hanyar amfani da ababen fashewa kuma sun ƙone takardu da wasu muhimman abubuwa ƙurmus a kotun.
Wasu mazauna yankin da suka leqa don gane wa idonsu yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa maharan sun lalata kusan ɗaukacin kotun.
Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike don kamowa da kuma gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
Ƙungiyar IPOB mai neman ɓallewa daga Nijeriya dai ta zafafa kai hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, musamman a Jihar Imo.
A baya-bayan nan hare-haren ƙungiyar sun yawaita a kan Ofisoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da kuma kotuna.
Rahoton INEC ya nuna sau tara aka kai wa ofisoshinta hari a Jihar Imo, baya ga wasu wurare a jimillar hare-hare 53 da aka kai wa cibiyoyin hukumar.
