“Adabi ba zai taɓa mutuwa ba har sai an wayi gari babu wanda ya rage a duniya”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wani salo da ya bambanta marubuta maza da mata, shi ne batutuwan da kowanne ɓangare ya fi mayar da hankali a kansa don faɗakar da al’umma. A yayin da a ɗaya vangaren akasarin marubuta mata ke rubutu kan batutuwan da suka shafi zamantakewar aure da rayuwa, maza sun fi baje basirarsu ne ta ɓangaren jarumta da almara ko abubuwa masu tsoratarwa, da kuma a wani batutuwan da suka shafi sarauta da siyasa. Ko da yake kowanne daga cikin waɗannan ɓangarori yana iya ninkaya a cikin salon ɗaya ɓangaren. Wani marubuci da yake rikiɗa a cikin salo daban daban, da muka ambata a baya shi ne Yusuf Yahaya Gumel, marubucin littafin ‘Gawa Da Rai’. A zantawarsa da wakilin Manhaja, Malam Yusuf ya bayyana masa irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya kai ga samun damar buga littafinsa na farko, da yadda kishin cigaban adabi ya kai su ga kafa Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Jigawa, (JISWA).
MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka.
YUSUF GUMEL: Sunana Yusuf Yahaya Gumel.
Ko za ka gaya mana taƙaitaccen tarihin rayuwarka?
Ni ɗan Jihar Jigawa ne, da a ka haifa a ƙaramar Hukumar Gumel. A shekara ta 1991. Na fara karatu daga na Muhammadiyya a wata makarantar Allo da ke unguwar mu har na kai matakin izifi biyu. Daga nan aka sanya ni a makarantar boko a wata Firamare da ke garin Gumel, da ake wa laƙabi da Nasoro Science Special Primary School. Bayan na kammala ƙaramar sakandire a shekarar 2007 na wuce babbar sakandire mai suna Government Day Secondary School Lautai, ita ma na kammala a shekarar 2010. Sai kuma na ɗora zuwa matakin Diploma, inda na karanci fannin koyarwa. Karatun boko bai hana ni cigaba da karatu na addini ba, kamar yadda hakan bai hana yin sana’a ta dogaro da kai ba. A taqaice ina jifan tsuntsu uku ne da dutse ɗaya. Kafin daga bisani na tsunduma harkokin kasuwanci na sayar da kayan shafe-shafe da kyale-ƙyale na mata. A yanzu haka ina dab da kuma cigaba da karatuna na digiri. Ina da aure mata ɗaya da kuma yaro ɗaya.
Wacce gwagwarmaya ka sha a lokacin karatunka da tasowarka, wanda ya taimaka wajen gina rayuwarka?
To, kamar yawancin mutane da ke duniyar nan dole a rayu da gwagwarmaya, sai dai ƙila ta zamo mabambanta ta fuskar tawa gwagwarmayar.
Na taso da jajircewa sosai da ƙwazon mayar da hankali ga cimma nasara a bisa abubuwan da na sanya a gabana, musamman karatu na boko da addini. Hakan yana daga cikin abin da mahaifana suka gina tunanina a kai cewa nasara ba ta samuwa ba tare da aiki tuƙuru ba, a hanyar nasara kuma dole a haɗu da ƙalubale iri-iri da wata rana za su zamo tarihi.
Ba wani abu ba ne da kowa zai gaza sani cewa a neman ilimi dole ne haɗuwa da barazana iri-iri ta duka, faɗa har ma da ta juriya a wajen haquri da kaɗan, wata rana ma a rasa. To, duk hakan ta faru da ni.
A ɓangaren sana’oi dogaro da kai kuwa na yi da yawa sosai. Misali sana’ar rake, sayar da kananzir, tallan ruwan leda da sauran su ba, sai dai hakan ya zamo tarihi yanzu, domin ko ba komai ina rayuwa cikin rufin asiri da godiya ga Ubangiji Allah bisa ni’imomin da ya mini na rayuwa. Babban abin da zan iya ƙarawa bai wuce ba a ƙarshe na ilimantu da waɗannan abubuwan a matsayin hanyar cimma nasara. Haƙuri, biyayya, gaskiya da amana da alƙawari, adalci.
Mai ya fara jan hankalinka kan rubuce rubucen adabi?
Abin da ya ja hankalina shi ne, sha’awa wadda ta tasirantu da karance-karance da na taso da shi na littattafai da yawa na marubuta, wanda har hakan ya kai matakin na zamo abin bayyanawa a gaban ɗalibai ‘yan’uwana na yi karatu a gaban aji a lokutan darasin Hausa. Wasu lokutan idan ina karatun ma har ya kawar da kai nake gefe na riƙa kawowa da ka.
Har ta kai ina iya tsara nawa labarin na bayar a baki a saurara a yi ta jinjina mini. A hakan wani malamina ya tava cewa da ni. “Yusuf, kana da baiwa ta ƙirƙira sosai, ina ji a raina wata rana za ka zama marubuci.” Ba a jima da maganar ba na fara rubuta wani labari mai suna Mutuwa Kusa, adabin yaqi ne, ni da wani abokina da a ke kiransa da suna Iliyasu Abubakar.
Wacce gudunmawa ka samu a lokacin da ka fara tunanin buga littafinka na farko?
Na samu ƙwarin gwiwa sosai daga iyayena, sai kuma mataki na gaba a duba mini aikin nawa kafin a kai matakin bugawa, wanda hakan shi ne ya dakusar da aikin, domin wanda na bai wa ɓatar da littafin ya yi an sha kai ruwa rana kafin a kai ga samunsa abin takaici! Bai duba komai ba.
Marubuta da dama na da tarihin matsalar kan-ta-waye, a tashin farko na fara fitar da littattafan su, wanne ƙalubale ka fuskanta?
Ni ma kamar kusan sauran marubuta Ina da wannan, a lokacin da na yi rubutun wajen shekarar 2006 ban san ta ya ake buga littafi ba da kuma hanyar da zan bi. Wannan ta sanya na shiga lalube ko zan samu wani da ke da sani a fagen hakan, a ƙarshe na yi kicibus da wani da ya ba ni shawarar zai fi na yi haƙuri na ajiye kayana kawai, domin dai shi ma da ya je an ce masa sai dai kawai ya sayar da littafin, wannan ya sanya ni jikina ya yi sanyi, sai na ji na sare gabaɗaya a haka na dawo na ajiye littafin, wanda a ƙarshe ma ya ɓata.
Daga ranar ban sake tunanin yin wani rubutu ba sosai har sai bayan samuwar wani dandali na marubuta a shafin fesbuk mai suna Duniyar Marubuta. Ta dalilin shi ne na qara samun damar dawo da burina na farko wanda na cigaba da rubuta labarai a yanar gizo ina sakarwa, masu yabo da suka na yi.
Littattafai nawa ka rubuta kuma ka fitar da su kasuwa, ba mu sunayen su da taƙaitaccen bayani game da wasu a ciki?
Na rubuta littattafai da yawa, da suka haɗa da, ‘Tsintacciya’, ‘Wani Dare’, ‘Zullumi’, ‘Ƙaddarar Rayuwa’, ‘Farautar Kuɗi’, ‘Baqƙar Farauta’, ‘Daren Mutuwa’, sai ‘Gawa Da Rai’. Wanda yake kasuwa a halin yanzu guda ɗaya ne, kuma ya fita ne a shekarar 2022 tare da dafawar babban abokina Barista Jibrin Rano, marubuci mai kishin marubuta.
To, shi dai littafin ‘Zullumi’ yana ɗauke ne da labari a kan wasu abokai uku da suka yi tarayya wajen aikata kisan kai na wata budurwa wadda aka musu alƙawarin miliyan biyar biyar kowanne. Sun aikata kamar yadda ake so su yi, sai dai kuma bayan an ba su kuɗaɗen a lokacin masifu suka fara bin su ɗaya bayan ɗaya.
Shi kuma littafin ”Gawa Da Rai”, labari ne na wani matashin saurayi da tunaninsa ke ginuwa a kan mutane suna masa kallon matacce, shi kuma a ɓangaren tunaninsa yana raye. Amsoshin yadda jumurxa suke yana cikin labarin da a yanzu haka yana kasuwa, akwai kuma PDF ga wanda ke buƙata, sai a tuntuve ni a wannan lambar waya, O7033189144.
Wacce nasara ko ɗaukaka za ka iya cewa ka samu ta dalilin rubutu?
Na samu nasarori masu tarin yawa, alhamdu lillahi. Na samu kusanci da mutane daban-daban wanda idan ba domin rubutu ba inuwarsu ma za ta mini wahalar kallo. Na samu nasarar gyara matsaloli da yawa ta fuskar rubutu wanda yawanci Ina jin hakan daga makaranta labaraina. Na samu daraja da matsayi har ma da girmamawa ga mutane daban-daban.
Wasu sun ziyarce ni, na ziyarci wasu na taka wurare da yawa sanadin rubutu. Na kuma samu kyauta ta kuɗi daga cin gasa, wasu kuma daga masoya, wata kuma daga mutane da yawa masu daraja.
Wanne abu ne ya tava faruwa da kai da har yanzu ba ka manta da shi ba a harkar rubutun adabi?
Abin da ya faru da ni shi ne, fitar labarina na farko wanda shi ne burina.
Wacce gudunmawa ka ke bayarwa ga cigaban adabi, yanzu da harkar ɗab’i ta ja baya?
Ina bayar da gudummawa sosai ga marubuta wanda suke a ƙasana ta fuskar gyara da shawarwari sosai, kuma Ina alfahari da cewa na dasawa mutane da dama sha’awar rubutu na kuma koyar da su dubaru na rubutu da kiyaye ƙa’idojin rubutu daidai gwargwado na sanina.
Koyaushe ƙofata a buɗe take ga marubuta daga ko’ina Ina bayar da tallafi domin ganin sun inganta ayyukansu sun kuma samu nasara. Da yawa kuma kwalliya na biya kuɗin sabulu domin dai na ga marubuta da dama da suna cikin wanda na bai wa gudummawa sun yi nasara a gasa sosai, sun kuma taka matakai da dama. A ɓangarena Ina ƙoƙarin ganin na ƙara ankarar da al’umma su fahimci adabi ba zai taɓa mutuwa ba har sai an wayi gari babu wanda ya rage a duniyar nan, domin dai yana tafiya ne da al’umma.
Wacce hanya za a bi a farfaɗo da harkar ɗab’in buga littattafai da inganta rubutun adabi?
A nawa hangen shi ne ta hanyar ƙoƙarin dasawa masu tasowa nan gaba sha’awa da romon da ke ɗauke da labarin da aka rubuta a littafi. Kodayake zamani kan sauya abubuwa su canja kamar a yanzu da giza-gizan sadarwa a ƙauli mafi inganci, ba kamar yanar gizo ba da a ke cewa, ta mamaye komai, waya ita ce abu mafi muhimmanci da kusan hannun kowa akwai, wannan shi ya sanya kasuwar littafin bugu ta yi ƙasa sosai, domin da yawan ‘yan zamanin nan ba sa iya karɓar wani abu da zai iya raba su da wayarsu na wasu lokutan.
A ganina ba za a iya dawo da martabar karatu a littafi ba har sai mutane sun bar yawan amfani da waya wanda hakan da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. Sai dai ko a yi amfani da batun Hausawa da suke gwada azancin magana na a jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ma’ana a inganta rubutun online sai kuma shi ma na bugawa a janyo hankalin mutane su riƙa biyun ya zamo ko’ina aka je dai akwai su.
Batun ingancin rubutu kuwa dole sababbin marubuta su yi karatu, su yi bincike, su yi nazari su kuma yi tambaya su zamo masu karɓar gyara. A ƙarshe ya zamo an wayar da kawunan masu karatu labarin da suka dace a karanta, lokacin da masu harbar ta mati a rubutu suka fahimci kan mage ya waye labaran da suke da tasiri sai sun zamo masu inganci, dole su zo su bi yarima a sha kiɗa da su, idan kuma ba haka to, a ƙarshe alƙiyamar rubutunsu ce za ta tsaya!
Wanne tallafi matasan marubuta na yanzu ke buƙata daga wajen tsofaffin marubuta?
Shawara ta dai shi ne su yi rubutu mai inganci, su kula da ƙa’idojin rubutu, su fahimci cewa nagartar marubuci ba a yawan littattafan sa take ba tana ga tasirin abin da ya rubuta mai kyau da nagarta da amfanarwa. A kuma riƙa fafutukar shiga lamuransu, akwai buƙatar a samu tsari na taimakon juna ta fuskar duk wani marubuci da ya fitar da labari ya zamo dandazon marubuta sun yi rubdugu da wasoson saya da karantawa. Hakan zai zamo ana samun ginuwa sosai kuma hakan zai sanya kowa ya ji yana sha’awar buga littafi zai kuma kula da ingancinsa sosai.
Marubuta sune suka san matsalarsu su ne za su fara mata magani. A karshe su kuma ƙananan marubuta su zamo masu biyayya su kuma sani cewa rubutu ba a yinsa da tunanin kuɗi, ko samun ɗaukaka lokaci ɗaya da sannu hakan ke zuwa a nan gaba.
Kana daga cikin shugabannin ƙungiyar marubuta ta Jihar Jigawa, ba mu labarin yadda aka fara tunanin samar da wannan ƙungiya?
Tunanin kafa JISWA ya samo asali ne daga taron Ranar Marubuta ta Duniya a garin Katsina. A lokacin da muka ci karo da marubuta da dama ‘yan Jihar Jigawa wanda suka zo daga mabambanta garuruwa, da a ƙalla mun kai mu biyar. Shugaban ƙungiyar na yanzu Hashim Abdallah, Jazuli Ya’u Hashim, da kuma Bello M. Bello sai kuma ni Yusuf Yahaya da kuma Abba Abdullahi Gumel.
A nan ne muka fara tattaunawa a kan me zai hana a samar da ƙungiyar marubuta da za ta taimakawa ƙungiyar marubuta ta ƙasa ta ANA a Jihar Jigawa. Da wannan tunanin muka dawo gida, muka kuma fara haɓɓaka shi tare da dafawar shugaban ƙungiyar na yanzu. Har kawo yanzu haka da ƙungiyar ta yi nasarar sanuwa a ko’ina a faɗin jihar kuma damfare take da mutane daga ɓangarori daban daban na Jihar Jigawa. Kuma a halin yanzu ina taka rawa a matsayin Mataimakin Shugaban qungiyar JISWA.
Wacce gudunmawa ƙungiyar marubutan Jihar Jigawa take bayarwa ga cigaban adabi?
A ɗaiɗaiku da matakin ƙungiya muna ba da taimakon da ya dace ta fuskar inganta rubutu da sauransu.
Ƙungiya Jihar Jigawa da a ke wa lakabi. Jigawa state Writers Association (JISWA) ta ƙyanƙyashe marubuta da dama daga cikin dukkan garuruwan Jigawa. JISWA
na shirya gasa ga marubuta da dama wanda take fitar da zaƙaƙurai sosai. Tana bayar da gudummawa ganin marubuci ko marubuciya ya ƙaddamar da littafinsa.
Wasu daga cikin sun samu nasarori da yawa da ɗaukaka a sanadin ƙungiyar.
Ana kuma ƙyanƙyashe mawaƙa sosai a cikin ƙungiyar da suke aiki dare da rana wajen wayar da kan mutane bisa abubuwan cigaba da ƙasa bakiɗaya.
A matsayin da nake ina taka rawa a dukkan nasarorin da ƙungiyar take samu. Ina ɗaya daga cikin jagororin da JISWA ke tafiya da tunaninsu a kai, wannan ta sanya abu ne sananne cewa marubuta, mawaƙa ko manazarta na cikin ƙungiyar ke girmama ni mutuƙa, kuma ba sa shakkar tunkarata da matsalolinsu musamman ƙananan marubuta da suke tasowa.
Yanzu haka na yi nasarar shigo da mutane sosai a cikin ƙungiyar kuma suna jin alfahari kasantuwa cikinta.
Wacce shawara ka ke da ita ga marubutan adabi na Jigawa?
Kira na gare mu shi ne mu haɗa kai mu zamo tsintsiya maɗauri ɗaya, mu kuma yi haƙuri da juna. Mu shigo cikin tafiyar domin bayar da gudummawa wajen ciyar da Jihar gaba. A cigaba da jajircewa a tallafar masu buƙatar tallafi. A cigaba da aiki cikin gaskiya da amana da kuma kishi.
Wanne mafarki ka ke da shi nan gaba ga bunƙasar rubutun adabin Hausa?
Mafarkina da burina, fatana shi ne marubuta su cimma nasarori masu tarin yawa da saƙonsu zai isa ga ko’ina za kuma a ga alfanunsu a ko’ina ina fatan wata rana a hango wasu daga cikin marubutan da na sani akan madafun iko na ƙasar nan, wanda hakan zai bayar da dama su gasgantar da burinsu da fatansu. Mafarkinsu a zahiri wa al’umma ta fuskar cimma nasarori a wajen da aka gaza suka kuma jima suna nuni da alƙalaminsu da ya zarta takofi.

Wacce rawa gwamnati da ýan siyasa za su iya takawa ga cigaban harkokin rubutun adabi?
Su shigo ciki su tallafa da damar su da ikonsu da kuɗinsu, su kuma fahimci cewa marubuta ‘yan kishin kasa ne da suke rayuwa a duniya su mutu da burin al’amura sun yi daidai ko sun yi kusa da daidai su sani marubuta na da iko da baiwar canja fari zuwa baƙi, ko mayar da baƙi ya zama fari. Ta hanyar rubutu kuma su fahimci ƙasashen da suka cigaba na duniya marubuta sune a gaba wajen bayar da shawarwari.
Ko ƙasar mu tarihi ba zai manta da manyan marubuta irinsu Abubakar Imam marubucin littafin Magana Jari Ce, wanda ya yi hidima iri-iri ga sarakuna lokacinsa har ma da gwamnatin lokacinsa da ƙasar mu ta Nijeriya. Marubuta suna buƙatar mutanen nan domin dai a gudu tare a kuma tsira tare.
Wanne abu ne ya faru da kai a matsayin ka na marubuci, wanda ba za ka manta da shi ba, na daɗi ko akasin haka?
Abin da ya faru da ni, shi ne irin yadda marubuta suke kusantuwa da ɗan’uwansu marubuci a lokacin farinciki, ko na baƙin ciki. Kuma mutuwar marubuci ba ya hana a manta da bayan da ya bari.
Wannan ta faru da dandazon marubuta suka yi tarayya wajen tallafawa iyalin marubuci Bello M. Bello Ringim. Allah jiqansa da rahama.
Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?
Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
Mun gode.
Ni ma na gode.
