2023: Da alama INEC ba za ta ci kasuwa da malaman jami’a ba

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Da alama Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shirya yin amfani da jami’anta a matsayin turawan zaɓe a zaɓen 2023 maimakon amfani da malaman jami’o’i kamar yadda ta saba a baya.

Majiya mai tushe daga hukumar ta shaida wa jaridar News Point Nigeria cewa, kawo yanzu ba a yi batun amfani da malaman jami’o’i a shirye-shiryen da INEC ke yi dangane da zaɓen na bana ba.

A cewar majiyar, “Kimanin kwana 40 kafin zaɓe ke nan amma ba a ce komai ba game da sako malaman jami’o’i a shirye-shiryen da hukumar ke yi.

“Da kamar yadda aka saba ne, kawo yanzu da an tuntuɓi malaman tare da tura musu wasiƙu, sannan shirin ba da horo ya biyo baya.

“Da yanzu jami’o’i sun aike da sunayen mayan jami’ansu ga hukumar don tantancewa, kuma babu wanda zai san inda aka tura shi har sai ranar zaɓe.

“Shugaban INEC da muƙarrabansa kaɗai za su inda aka tura jami’an, amma ga shi har yanzu babu komai game da hakan,” in ji majiyar.

Majiyar ta ƙara da cewa akwai yiwuwar a saka jami’ai bibbiyu da za su yi aikin tattara sakamakon zaɓe a cibiyoyin zaɓe 8809 da ake da su a faɗin ƙasa.

”Bari dai mu jira mu gani, zaɓen wannan shekarar na tattare da abubuwan mamaki,” in ji majiyar.

By Editor