Mutane da dama ake zargin sun maƙale a bene mai hawa ukun da ya rushe wanda ba a kammala aikin gina shi ba a yankin Gwarimpa da ke Abuja.
Majiyarmu ta ce iftila’in ya ritsa da ma’aikatan da ke aikin ginin.
An ga jami’ai daga hukumomi daban-daban a wurin da lamarin ya auku inda suke ƙoƙarin aikin ceto.