Ya kamata maza su taimaka wa matansu a ayyukan gida da na aiki – Larai Binta Hassan

“Mata na da ilimin lissafi, ilimin tsumi da tanadi da binciken kuɗi, rashin goyon baya ne ke hana su aikin banki”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gimbiyarmu ta wannan makon ƙwararriya ce a harkar zamantakewa da aikin banki, tana da ƙwarewa a harkar shige da ficen kuɗaɗe da tattalin kuɗi. Sannan mace ce mai kishin cigaban rayuwar mata da yara mata marasa galihu da ke neman wanda zai tausaya musu su samu ilimi da kyakkyawar rayuwa. Ta amfanar da mata da marayu masu yawan gaske, ƙarƙashin ƙungiyarta ta Motherhen Initiative. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya zanta da ita kan rayuwarta da kuma burinta na ganin kyautatuwar tarbiyyar ýaýa mata da matasa.

MANHAJA: Muna son ki fara da gabatar mana da kanki.

HAJIYA BINTA: Cikakken sunana dai Larai Binta Hassan. Na fito daga iyalin Alhaji Bala Namaifulani da Hajiya Hauwa Talatu Bala Namaifulani. Mahaifina asalin sa mutumin Jihar Sakkwato ne, mahaifiyata kuma ýar asalin Jihar Yobe ce. Ni tsohuwar mai aikin yaƙi da shaye shayen miyagun ƙwayoyi ce, kuma tsohuwar ƙwararriyar ma’aikaciyar banki. Ni ce shugabar ƙungiyar tallafa wa mata da ƙananan yara ta Motherhen Initiative. Sannan kuma har wa yau ni ýar kasuwa ce, mai sana’ar harkokin noma da kiwo.

Menene taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
An haife ni a Anacha, wato Onitsha da ke Jihar Anambra ta yanzu, wajen shekaru hamsin da ‘yan kai. Mahaifina ɗan kasuwa ne da yake gudanar da kasuwancin sa tsakanin Arewa da Kudu. A sakamakon ɓacewar yaƙin Biyafara ne sai iyayena suka koma da zama Jos, a nan aka sani a makarantar firamare ta Saint Theresa a nan Jos. Sannan na wuce Kwalejin Ýan mata ta Tarayya ta FGGC da ke Bauchi inda na yi sakandire.

Daga nan na je makarantar nazarin aikin kimiyya da fasaha ta ‘School of Arts and Science’ da ke Jihar Sakkwato, inda na yi karatun gaba da sakandire, daga nan ne kuma na koma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na samu digirina na farko a fannin ilimin sanin zamantakewa, wato ‘Sociology’. Na kuma yi hidimar ƙasa a Ƙaramar Hukumar Ɓilliri da ke ƙarƙashin Jihar Bauchi a wancan lokacin, yanzu kuma tana Gombe, a shekarar 1989.

Sai bayan da na gama ne na yi aure a watan Disamba na wannan shekarar. Sai a shekarar 1990 na sake komawa makaranta inda na yi karatu digiri na biyu duk dai a ɓangaren zamantakewa, wannan karon a Jami’ar Jos na yi. Ina cikin yin karatun ne na samu aiki da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, wato NDLEA lokacin da aka kafa ta sabuwa, na yi aiki a shashin faɗakarwa da rage amfani da miyagun ƙwayoyi.

A shekara ta 1994 na bar aiki da NDLEA ba don son raina ba. Amma yadda Allah ya ke abin sa a 1995 na samu aiki da First Bank PLC a nan na yi aikin shekaru 26 har na yi ritaya a shekarar 2021.

Na riƙe muƙamai daban daban da suka haɗa da manajan banki mai kula da reshen First Bank a majalisar ƙasa, ni ce na fara buɗe wannan reshen. Daga nan na riƙe muƙamai na Manajan Reshen titin Ahmadu Bello da ke Abuja, da na reshen Garki da reshen Central Area na Asokoro.

Na kuma ƙarƙare da muƙamin Manajan Yanki, wato ‘Regional Manager’ mai lura da rassan First Bank a jihohin Filato, Benuwe da Kwara. Na yi ritaya a ofishina a Jos.

Waɗanne abubuwa ne za ki ce mu’amalarki da mutane ta sa ki gogewa da rayuwa?

Da farko dai Babana Alhaji Bala Namaifulani (Allah Ya yi masa rahama) attajiri ne. A zamansa a Anacha da tafiye tafiyensa na kasuwanci a cikin Najeriya da kewaye ya yi abokantaka da mutane iri iri. Saboda haka za ka ga cikin abokanensa akwai Hausawa, akwai Ibo, akwai Yarabawa, da dai sauran ƙabilun Najeriya da makwaftan ƙasashe, a haka muka taso.

Ko a makarantar firamare har zuwa jami’a da lokacin aiki duk za ka ga mu’amala ta da jama’a babu wariya. Kuma tun daga gida na san cewa, akwai mutanen kirki da mutanen waɗanda ba na kirki ba. Saboda haka da fuskar da mutum ya zo maka da ita za ka karɓe shi har sai ya nuna maka wata fuskar daban.
Haka zalika a wurin aiki za ka yi mu’amala da kwastomomi, da na ƙasa da kai da kuma na sama da kai. Za ka haxu da nagari da masu neman su cuce ka ko wurin aikinka. Yarda da Allah, Iliminka, da asalinka, da kuma kwasa-kwasai da ka yi suke taimaka wa ka goge kuma ka yi nasara a rayuwa.

Ko za ki iya tuna wasu muhimman abubuwa da suka faru a rayuwarki, da suka mayar da ke Hajiya Larai a yau?

Na farko dai shi ne girma a hannun iyayena. Na koyi halin zamantakewa da mutane da kuma halaye na dattako, jin ƙai da tausayi.

Na biyu, shi ne samun abokin zama na gari mai tsoron Allah, wato maigidana Injiniya Sa’idu Hassan, wanda yake mara min baya, da bani shawarwari da kuma taimakawa, wajen samun sauqi a ayyukana na gida da na waje. Na uku, shi ne iyalai da abokai na kusa da na nesa masu nuna so da ƙauna.

Na huɗu, aiki da shugabanni irin na da, waɗanda suka yarda da cewa mata na da ýan cin cigaba a wurin aiki, kuma ya kamata a taimaka masu, a ba su damar yin haka. Akwai ƙarancin su a yanzu.

Yaya ki ke kallon rayuwa a da da kuma yanzu?

Rayuwar da akwai tsoron Allah, akwai yarda, da tausayi da taimakon juna da zumunci. Yanzu mun samu kanmu a wani yanayi da duk waɗannan kyawawan halaye sun yi ƙaranci. Akwai ƙarancin tsoron Allah, ƙarancin yarda da juna, ƙarancin tausayi da ma ƙarancin taimako. Son kai ya yi yawa. Yawan zargin juna ya haddasa wani yanayi na mutum bai jin daɗin zama sai a cikin ‘yan’uwa masu ƙabila ɗaya da addini ɗaya. Amma muna addu’a Allah ya kawo sauƙi.

A matsayin ki ta wacce ta yi aiki da NDLEA, wacce gudunmawa ki ke ganin za ki iya bayarwa don shawo kan yawaitar shaye shaye a tsakanin matasa, musamman ýan mata?

Faɗakarwa game da illar barin yara mata suna mu’amala da abokanen da kasan cewa ba su da hali na ƙwarai da kuma faɗakarwa game da illar shaye shaye da abinda ya kamata a yi don neman taimako. Idan mutum ya samu kansa a halin jarrabar amfani da miyagun ƙwayoyi.

Yaya ki ke ganin cigaban da shugaban hukumar NDLEA na yanzu ya kawo a ayyukan da hukumar sa ke gudanarwa?

Idan ka dubi tarihin Janar Muhammadu Buba Marwa za ka ga ya yi karatu a ciki da wajen Najeriya. Bayan haka da yake gwamna a Legas ni ma a lokacin Ina aiki a Legas ya taimaki wannan jihar ba kaɗan ba. Saboda haka da na ji an naɗa shi shugaban NDLEA na ce lallai ga gatari zubin aiki, domin ba shakka tarihin ya shaida ne. Yana aiki ba sani ba sabo. Sai dai mu yi masa addu’ar Allah Ya kare shi ya ƙara masa basira.

Yaya ki ke kallon gwagwarmayar mata ma’aikata da harkokin iyali?

A nan zan ce mata sun jajirce a wannan. Kuma suna tasiri a wurin aiki domin yanzu abubuwa sun zo da sauƙi. Amma fa ga wanda take da abokin zama mai taimaka wa kuma ta fahimci dabarun tsara iyalai da tsarin aiki.Wanda ya gane wannan komai zai tafi daidai.

A zamanin yanzu aure ya zama taimake ni na taimake ka, saboda haka abokanen zama ya kamata su taimaka wa mata su samu sauƙi a ayyukan su na gida da na aiki. Su ma matan su samu kwanciyar hankali da nutsuwa, su cimma burin su na rayuwa.

Wanne ƙalubale mata masu aikin banki suke fuskanta a wajen aiki da cikin jama’a?

Babban ƙalubalen shi ne, samun goyon bayan iyalensu domin aikin banki ya na buƙatar lokacin da hulɗa da jama’a, don akwai wasu abokan zaman da ba sa yarda da haka, shi ne babban ƙalubalen. Domin mata su na da Ilimin lissafi, ilimin tsumi da tanadi, ilimin tattalin kuɗi da binciken kuɗi waɗanda sune ake buƙata a aikin banki. Saboda haka muhimmin abin shi ne goyon baya.

Wacce gudunmawa ƙungiyar ki ta Motherhen Initiative take bayarwa ga cigaban rayuwa?

Gudunmuwar da MotherHen Initiative ta ke bayarwa sun haɗa da tallafa wa mata masu ƙaramin ƙarfi, tallafa wa almajirai da marayu, da taimaka wa yaran mata ta fannin cigaban iliminsu.

Menene dalilin ki na kafa ƙungiyarki ta Motherhen Initiative?

Dalili na shine, yadda na ga ƙuncin rayuwa da yadda masu ƙaramin ƙarfi suke fafutuka a rayuwa, da muhimmancin haɓɓaka ilimin yara mata da ke buƙatar a taimaka musu.

A lokacin da nake fafutukar kafa ƙungiyar na yi shawara da mijina wanda shi ne babban aminina, na yi shawara da iyalina, da kuma surukina Alhaji Sani Mu’azu. Da taimakawar su da shawarwarin su muka kafa wannan ƙungiya na ba da tallafi da taimako.

Daga ina ki ke samun tallafin kuɗaɗen gudanar da ayyukan da ku ke yi?

A yanzu dai daga aljihunmu ne, wato aljihun mu daraktocin da muke gudanar da MotherHen Initiative. Amma, Ina da tunanin nan gaba za mu haɗa hannu da wasu ƙungiyoyi masu manufofi irin namu da masu hannu da shuni da su zo mu haɗa hannu mu cimma burin ɗaya.

A matsayin ki ta uwa, yaya ki ke kallon yadda tarbiyyar iyali take taɓarɓarewa?
Tavarvarewar tarbiyya gaskiya abu ne da ya addabi iyalai da yawa. Ita tarbiyya tun daga gida ake kafa ta. A da ba mu da na’urorin rayuwa kamar yadda ake da su yanzu.

Saboda haka mu’amalarka da abokanka da iyaye da maƙwabta kawai ka sani. Kuma shi ne iyaye suke sa wa ido su yi maka gyara a inda ka yi kuskure. Na tuna muna yara idan aka kawo ƙarar mu, mahaifiyata ta kan ce wa mai ƙarar ai ba ki yi daidai ba, da kin rako ta da bulala ne da na yi murna. Bayan an sarrafa ka sai a tambaye ka za ka sake? Ka ce a’a, sai a tambaye ka, idan ka sake fa? Kai za ka bada amsar abin da za a yi maka. Dole mu nutsu mu san ya kamata.

Amma yanzu an bar wa ýan aiki lura da tarbiyyar yara. Ko iyaye na nan ana can ana kallon Zee World da makamantan su. Uba na can wajen nema to, wa zai sa wa yara ido? Wani lokacin ma ka ga yaro ɗan karami ana nuna masa so a ba shi babbar waya a sa masa data ya kunna ya kalli abinda yake so ba mai kula da abinda ya ke ciki.

An ce itace tun daga ƙarami a ke tanƙwasa shi. Sai ka ga yara sun tashi da ra’ayoyin da suka tsinta na wasu mutane can waɗanda addininmu da al’adunmu ba iri ɗaya ba, mu namu an mai da su marasa amfani. Ba wanda ya damu da inda yaro za shi ko ina ya fito. Sai abu ya lalace a soma neman mafita lokacin kuma an yi latti. Gaskiya sai mun tashi haiƙan mun yi gyara .

Waɗanne abubuwa ne za ki so a danganta ki da su, a matsayin cigaban da ki ka samu na rayuwa?

Zan so a danganta ni da taimakawa wurin haɓɓaka ilimin waɗanda na yi aiki da su, da na ‘yan uwa da abokai. Da tsayawa waɗanda aka nemi a zalunce su, da ayyukan taimakon jin qai da nake cigaba da yi har yanzu, har zuwa ƙarshen rayuwa ta.

Yaya batun iyali?

Ina da aure, sunan mijina Injiniya Sa’idu Hassan. Ina da yara uku biyu maza, ɗaya mace.

Menene ya fi faranta miki rai?

Ganin ana taimaka wa jama’a musamman masu ƙaramin ƙarfi.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Kowa ya yi nagari, kansa!

Mun gode.

Ni ma na gode.