Daga WAKILINMU
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga shugannin ɗarikar Tijjaniyya da kuma iyalan mabiya ɗariƙar su 19 da aka kashe a ƙasar Burkina Faso.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutanen ne ‘yan Nijeriya a ranar Laraba a kan hanyar su ta zuwa ƙasar Senegal domin ziyara.
A wata sanarwa da mai taimakawa Asiwaju Tinubu a kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu, ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna baƙin cikin sa kan abinda ya faru.
“Wannan abin baƙin ciki ne a ce mutane basu ji ba basu gani ba za a tare su hanya a hallaka su kai tsaye. Dole ne a bi diddigi wannan magana domin bi musu haƙƙinsu,” in ji shi.
Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga dukkanin shugabannin Tijjaniyya na Nijeriya, da iyali da ‘yan uwan mamatan.
“Ina kuma kira ga ma’aikatar ƙasashen waje ta ƙasa da ofishin jakadanci Nijeriya a Burkina Faso da su gaggauta bincike kan wannan al’amari domin ganin an hukunta waɗanda suke da hannu a ciki da kuma bi wa iyalan mamatan haƙƙinsu,” in ji shi.
Ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu ya kuma ba wa iyalansu haƙurin jure rashin.
