Daga BASHIR ISAH
A ranar Laraba Kotun Ƙoli ta dakatar da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na daina amfani da tsohuwar Naira daga ranar 10 ga Fabrairu, 2023.
Tawagar alƙalai bakwai ƙarƙasbin jagorancin Mai Shari’a John Okoro ne suka yanke wannan hukuncin biyo bayan ƙarar da gwamnonin Kaduna da Kogi da Zamfara suka shigar.
Kowacce daga jihohin da lamarin ya shafa ta shigar da ƙara inda ta nemi kotu ta dakatar da Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Bankin Ƙasa (CBN) ko kuma sauran bankuna daga matakin da aka ɗauka na daina karɓar tsohuwar Naira (200, 500 da 1000) daga ran 10 ga Fabrairu.
Da yake bayani a gaban kotun, lauyan masu shigar da ƙarar, Mista A. I. Mustapha, SAN, ya buƙaci kotun da ta amince da buƙatar da aka gabatar mata don tabbatar da adalci da kuma walwalar ‘yan Najeriya.
Ya ƙara da cewa, matakin da gwamnati ta ɗauka ya haifar da matsi wanda ke neman haddasa mulkin kama karya a ƙasa.
Lauyan ya ci gaba da cewa ƙididdigar (CBN) ya nuna sama da kashi 60 na ‘yan Najeriya ba su da asusu a banki, sannan ƙalilan da ke da asusun ba su zamun zarfin cire kuɗaɗensu.
Haka nan, ya muddin kotun ba ta shiga lamarin ba, hakan zai haddasa mulkin kama karya a ƙasa.
