Gidauniyar Yadudu ta gudanar da taron faɗakarwa karo na 12 kan illolin cutar hanta

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An gudanarda taron ƙarawa juna sani na shekara na Marigayi Kyaftin Isma’ila Auwalu Yadudu akan illolin cutar hanta ƙarƙashin waƙafin Gidauniyar Yadudu.

Taron an gudanar da shi a ranar Lahadi a ɗakin taro na gidan Mambayya da ya samu halartar mutane da dama.

Da yake bayani ga manema labarai shugaban kwamitin amintattu na Waƙafin Gidauniyar Yadudu. Farfesa Auwalu Hamisu Yadudu ya ce taron na yi wa jama’a bayani ne na wasu abubuwa dake tattare da cutar hanta don a faɗakar a jawo hankali akan abinda za a guda dake jawo cutar da kulawa da yin rigakafi.

Ya ce sun ware wuri ana gwada mutane wanda ke da alamun kamuwa da cutar sai ya je asibiti amma ba sa ɗaukar nauyin maganta cutar su dai suna bada damar a tantance mai cutar ne.

Farfesa Auwalu Yadudu ya ce babban abinda ya sa suka kafa wannan gidauniyar ta waƙafin Yadudu shine akwai ɗansu Kyaftin Isma’ila da Allah ya karɓi ransa a sanadiyyar cutar hanta duk da dai ba mai tsananin ba ne.

Kuma kafin rasuwarsa yana da sha’awar ya ga ana faɗakarwa a jawo hankalin mutane da wayar da kan mutane da tantance cutar don mutane su ɗauki matakin magani da rigakafi, kafin rasuwarsa ya bar wasiyya aka cigaba da yi.

Ya ce wannan shine taro karo na 12 amma shekara 15 kenan da kafa gidauniyar an samu tsaiko a baya a sanadin annobar cutar sarƙewar numfashi shi ya sa ba a yi ba.

Ya ce da farko suna yin gwaji ga mutum 250 amma yi na huɗu da suka gabata suna yi wa mutane 400, wannan karon ma 400 aka yi a cewarsa.

Ya ce akwai makamantan taruka da suka yi a Dawakin Kudu shekara uku ana yi wanda shi wannan har da kula da yara jarirai da wanda ba su kai shekaru biyar ba.

Auwalu Hamisu Yadudu ya ce data ayyukansu akwai taimakawa mata da gina makarantar Islamiyya da haƙa rijiyoyin burtsatse an yi har a wajen Kano an yi a Funtuwa, Katsina da sassa da dama.

Shi ma wanda ya gabatar da jawabin faɗakarwa akan cutar hanta Farfesa Adamu Alhaji Sama’ila ya bayyana hanyoyi da ake kamuwa da cutar da dama da yanda za a yi kariya ya kuma yi kira ga mutane akan su riqa zuwa ana gwadasu su san matsayinsu akan cutar don ɗaukar mataki.

Ya yaba wa ƙoƙarin waƙafin Gidauniyar Yadudu da take gudanar da wannan taro karo na 12 da sunan Marigayi Kyaftin Isma’ila Yadudu wanda haziƙin soja ne da aka yi rashinsa shekara 15 da suka gabata.

Ya ce an cimma nasara sosai sanadin irin wannan taron ƙara wa juna sani wajen mutane da dama sun san matsayinsu akan cutar sun ɗauki mataki na magani wasu kuma an yi musu rigakafi.

Farfesa Adamu Alhaji Sama’ila ya ce gidauniyar ta yi abubuwa da dama wajen wayar da kan al’ummar Kano da maqota kuma tana ɗaukar nauyin bai wa mutane a tantance su akan cutar kyauta.

Shi ma ɗaya daga cikin amintattun waƙafin Sadiq Labbo Sharubutu ya yi kira ga al’umma masu hali su koyi irin wannan a sashen da suke da tasiri akai ko kasuwanci, noma, aiki ko koyarwa mutum ya samu na kusa da shi su yi tunanin abinda za su yi ya amfani al’umma.

Ya ce shekara 12 kenan ana wannan hidima yin irin wannan komai ƙanƙanta zai yi amfani.

Alhaji Sadiq Labbo Sharubutu ya ce ba ƙaramin hidima ake ba kafin a haxa taron amma juriya da ake da tsayawa kai da fata shi ya sa ake samun nasara suna fata Marigayi Kyaftin Isma’ila Yadudu da mahaifiyarsa da ake abin ɗansu Allah ya jiƙansu.

A yayin jawabinta na godiya a madadin waƙafin Gidauniyar Yadudu, Amal Isma’ila Yadudu ta yi fatan Allah ya jiƙan waɗanda aka assasa gidauniyar ɗansu ya sakawa waɗanda suka yi ɗaiwainiyar gudanar da taron da mahalarta taron da alkhairi.

By Editor