*Kotun soji ta samu Janar Muhammed da laifin karkatar da miliyoyin Dala
Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Majalisar Dattawan Nijeriya ta ƙuduri aniyar yi wa hafsoshin tsaron ƙasar kiranye, saboda taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, musamman Arewacin Nijeriya.
Majalisar Dattijai ta ɗauki matakin ne a jiya Alhamis bayan tattaunawa kan batutuwan yin garkuwa da wasu ɗalibai mata guda biyar na Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma dake Jihar Katsina a ranar Laraba bayan da Sanata Yar’Adua mai wakiltar yankin Katsina ta Tsakiya a majalisar ya gabatar da ƙudirin.
Waɗanda za a gayyace sun haɗa da; Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da Shugaban Hafsan Sojin Sama, Air Marshall Hassan Abubakar.
Sauran waɗanda za a gayyata sun haɗa da; Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olukayode Egbetokun da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
’Yan majalisar sun buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an kuɓutar da ɗaliban mata da aka sace da kuma sauran waɗanda da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.
Sun bukaci sojoji su gudanar da ayyuka na musamman domin fatattakar ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan.
Sanatocin sun kuma jaddada buƙatar samar da ‘yan sandan jihohi a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.
Har yanzu ba a ƙayyade ranar da aka shirya yin ganawar da hafsoshin tsaron ba.
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne suka yi awon gaba da ɗaliban jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke jihar Katsina, aqalla biyar, inda ’yan sanda suka tabbatar da kama ɗaya da ake zargi da hannu a lamarin.
Kotun sojoji:
A wani labarin da ya shafi matsalar tsaro mai alaƙa da cin hanci da rashawa kuwa, kotun sojojii ta musamman da rundunar sojin Nijeriya ta kafa ta samu tsohon Manajan Darakta kuma Mataimakin Shugaban Kamfanoni Mallakar Sojojin Nijeriya, Manjo Janar Umar Mohammed da laifuka 14 cikin 18 da suka haɗa da sata da sauran laifuka daban-daban, waɗanda dukkansu sun sava wa dokokin aikin soja.
Abubuwan da ake tuhumar Janar ɗin sun haɗa da sata, ayyukan jabun, haɗa baki, karkatar da kadarorin sojoji ba tare da izini ba, da dai sauransu.
A ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da aka same shi da shi, Janar Mohammed ana zarginsa da karɓar kuɗi dala miliyan 1.045,400 da kamfanonin sufurin jiragen ruwa suka biya domin amfani da Jetty na Sojojin Nijeriya da ke lamba 6 Marina, tsibirin Victoria da ke Legas.
An kuma same shi da laifin satar dala 430.800 na kuɗaɗen da aka biya a asusun ajiyar Sojojin Nijeriya da ke bankin Unity, Abuja don amfani da Jetty na Sojojin Nijeriya, Marina, Legas.
Kotun sojin ta kuma same shi da laifin janyewa tare da kwace maquden kuɗaɗe har Naira miliyan 74 daga cikin Naira miliyan 75 da aka biya na wani kadarori na sojojin Nijeriya da ke Ikoyi a Legas.
Sai dai an samu Janar din ba da laifi ba a kan zargin da ake masa na sayar da kadarorin Sojoji da ya kai Naira miliyan 200 a Legas tare da sace wasu Naira miliyan 750 daga cikin Naira Biliyan 2.5 da aka samu a bankuna da kuma gudunmawar da aka samu daga masu biyan kudin gidaje na sojoji da ke Asokoro a Abuja.
Har ila yau, ba a same shi da laifin yin akan jabun takardar yarjejeniya ba, bisa zargin kwace wani kadarorin Sojoji a Legas.
Kotun Soji ta musamman tare da Manjo Janar Kames Myam a matsayin shugabanta, tana da wasu Manjo Janar guda bakwai da kuma Birgediya Janar a matsayin lauya kuma ana sa ran za ta karanta hukunce-hukuncen da ta yanke wa waɗanda ake tuhuma a ranar Talatar makon gobe.
A yayin zaman kotun, an shigar da Manjo Janar U. M. Mohammed cikin kotun a keken marasa lafiya, amma shugaban kotun, Manjo Janar Myan ya ce, an gudanar da duk binciken da ya dace kan wanda ake tuhuma kuma duk sun tabbatar da cewa, ya cancanta a gurfanar da shi gaban kotu.
Babban Lauyan masu gabatar da ƙara shine Kanar BA Oguntayo (Mai Ritaya), yayin da Jagoran Lauyan Tsaro ya kasance Olalekan Ojo, SAN.
