Chicago: Zan dangana idan Kotun Ƙoli ta tsarkake Tinubu – Atiku

*Ɗan takarar PDP ya ce ba don kansa yake wa Tinubu tone-tone ba
*Siyasarka ta zo ƙarshe – APC ga Atiku
*Ba na tsoro domin Buhari ya gama kassara kasuwancina a Nijeriya, inji Atiku

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Ɗan takarar babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi iƙirarin cewa, idan har Kotun Ƙolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu tsarkakke ne shi, duk da satifiket ɗin da shi Atikun ya amso daga Jami’ar Chicago dake Birnin Ilinious, don ƙalubalantar sahihancin zaɓensa a 2023, to zai dangana ya haƙura ya mayar da komai ga Allah ba tare da ya ƙara tayar da jijiyar wuya ba, don alfanun ƙasar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin ne daga Atikun yayin gudanar da taron manema labarai na duniya da ya kira jiya Alhamis a Ɗakin Taro na Cibiyar Yar’Adua dake Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, inda ya ce, ba yana yin wannan jayayyar da Tinubu ba ne, don yana qin sa ko kuma don kansa yake yi ba, illa don tsarkake dimukraɗiyyar Nijeriya da ƙwato ta daga hannun ’yan gangan. Don haka ya ja tunga har sai ya ga abinda ya ture wa buzu naɗi.

“Ban shirya janyewa daga wannan gwagwarmaya ba,” inji Atiku, wanda ya ƙara da cewa, hakan ba cin zarafi ko butulci ne ga Tinubu, illa dai kawai mutuncin Nijeriya ne ke neman zubewa a idon duniya, saboda irin bayanan da ya samu kan takardun makarantar Tinubu na jami’a a Amurka.

Don haka sai ya yi kira ga sauran waɗanda suka tsaya takara a Babban Zaɓen na ranar 25 ga Fabrairu, 2023, Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Peter Obi na Jam’iyyar LP, da su zo su haɗa hannu waje guda, don ceto Nijeriya.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da Tinubu ne a matsayin wanda ya lashe zaɓen, amma sai Atiku da Obi suka garzaya kotu suna masu ƙalubalantar zaven.

Amma Kotun Musamman ta Zave a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani ta yi watsi da ƙarar, lamarin da ya tilasta wa Atiku da Obi ɗin ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Qoli, inda kuma a farkon makon nan ne wata kotun Amurka ta umarci Jami’ar Jihar Chicago da ta bai wa Atikun takardun karatun Tinubu, don ya gabatar da su a gaban Kotun Ƙolin a ƙoƙarinsa na tabbar wa shari’a da cewa, Shugaban ƙasar ya yi ƙarya a bayanan karatun da ya bai wa INEC, wanda idan hakan ta tabbata, to bai cancanci tsaya wa takarar ba kenan, lamarin da zai iya sanya kotun ta ayyana Atiku a matsayin wanda ya lashe zaven, saboda kasancewarsa wanda ya zo na biyu a yawan ƙuri’a.

Tinubu ya yi iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya hana jami’ar bayar da takardun, amma a ranar Litiinin da ta gabata jami’ar ta damƙa wa Atikun takardun, kamar yadda kotun majistare da ta gunduma a Amurka suka umarta.

A yayin taron Atiku ya ce, “na riga na shigar da ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli. Har sai ta yanke hukuncin cewa ya cancanta ne zan jingine bibiyar da na ke yi. Ma’ana; zan haƙura da ƙarar tawa idan kotun ta yanke hukunci, domin babu wata kotun da ta fi Kotun Ƙoli.”

A yayin da yake tabbatar da zargin an nemi a turo masa wasu mutane, don ya janye ƙarar da yake yi, Atiku ya ce ya lura da hakan, amma ya ƙi yarda ya ga mutanen, yana mai cewa, “Ban ma bar su sun zo gidana ba.”

Yayin da manema labarai suka yi masa tambaya kan ko a shirye yake da ya yi asarar harkokin kasuwancinsa a Nijeriya sakamakon wannan jayayya da yake yi, sai ya ce, ai da ma tuni tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kassara harkokin nasa.

Ya ce, “ba na tsoron ko za a daƙile min kowane irin kasuwancina. Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari ya riga ya daqile su ta hanyar janye lasisin dukkan kamfanonin da na mallaka tare da wasu.”

Daga na sai ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a Nijeriya ta fannonin addini, yanki, ƙabila, siyasa da sauransu kan su zo su haɗa hannu da shi, don a ceto Nijeriya.

APC ta rama wa Tinubu ranƙwashi:

Jam’iyya mai mulkin Nijeriya, APC, ta yi watsi da iƙirarin da Atiku ya yi, tana mai kira da ya janye ɗaukaka ƙarar da ya yi, domin siyasarsa ta zo ƙarshe daga wannan karon.

Jami’in Yaɗa Labaran Jam’iyya na Ƙasa, Felix Morka, ne ya yi kira jiya a yayin da yake magana a shirin Barka da Safiya na gidan talabijin na Arise.

Ya ce, “sakamakon da ya fito daga Jami’ar Chicago shine wanda dai muka sani tun tuni cewa, Shugaban Tarayyar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya halarci jami’ar ta Chicago a matsayin ɗalibinta.

“Rantsuwar Magatakardan Jami’ar a kotun Amurka ta tabbatar da hakan, saɓanin ƙalubalen da ɗan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke yi a gaban kotunan zaɓe. Muna masu farin ciki da sakamakon.

“Siyasar Atiku Abubakar ta zo ƙarshe. Rana ta faɗi masa. Ina tunanin ya gane hakan. Ya bauta wa ƙasar a matsauin Mataimakin Shugaban Ƙasa da sauran muƙamai. Hakan ya ishi mutum a cikin ƙasar nan, musamman wanda yake ɗan siyasa ne. An gode masa, amma yana buƙatar hutu haka nan.”