Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaryata labarin ƙarya da ake yaɗawa na cewa, ya kashe sama da Naira miliyan 400 a balaguro zuwa ƙasashen waje.
Rahotanni sun nuna cewa, wata jarida ta yanar gizo ta yi kuskuren ruwaito Gwamna Dauda ya kashe Naira 170,276,294.31 wajen tafiye-tafiye na ƙasa da ƙasa, N221,567,094 kan tafiye-tafiyen cikin gida, N6,929,500.00 kan harkokin tsaro na sirri cikin watanni uku.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce wasu vata gari ne suka ƙirƙiri labarin da gangan domin su ɗauke hankalin gwamnati.
Ya bayyana cewa wannan rashin fahimta ya samo asali ne daga kuskuren fassarar bayanan kasafin kuɗi da gangan, inda ya ƙara da cewa kashi na ɗaya da na biyu da na uku sun faɗa ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “Mun karanta wani rahoto da ke zargin Gwamna Dauda Lawal ya kashe sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje. Wannan ƙarya ce kuma yunƙurin ɓata sunan gwamna ne.
“Gaskiya da riqon amana sune ginshiƙin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal. Ana iya samun dukkan bayanan da suka dace a gidan yanar gizon gwamnatin jihar Zamfara a zamfara.gov.ng.
“An buga a shafin yanar gizon hukuma cikakken rahoto kan yadda ake gudanar da kasafin kuɗi, wanda ke ba da cikakken bayanin yadda Gwamna ke kashe kuɗaɗe a tafiye-tafiye da sauran ayyuka. A ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal, mun aiwatar da wani tsari na gaskiya da riqon amana, ba tare da barin wurin yin amfani da kuɗi ba.
“Don haka yana da kyau a fayyace cewa Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje sau uku kacal tun bayan da ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. Ziyarar ukun da ta yi zuwa ƙasashen waje ita ce: halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) a Amurka; wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya na ci gaba (UNDP) a Kigali, Rwanda; da kuma ganawa da shugaban bankin raya Afirka Dr Akinwumi A. Adesina a birnin Abidjan na ƙasar Cote d’Ivoire.
“Bugu da qari kuma, qƙungiyar gwamnonin Nijeriya ce ta shirya taron da aka yi a Kigali kuma hukumar ci gaban Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP ce ta ɗauki nauyi. Don haka babu wani kuɗi da gwamnati ta kashe a kan haka. Kuɗaɗen da aka kashe a tafiye-tafiyen ƙasashen waje shi ne na UNGA a Amurka, da kuma taron Gwamnan Arewa maso Yamma da Shugaban AfDB a Abidjan.”
Sanarwar ta ce: “Rahoton ya yi kuskure ya danganta kuɗaɗen da gwamnatin da ta gabata ta kashe kuɗaɗen da gwamnatinmu ta yi. Gwamnatinmu ba ta taba daukar jami’an tsaro masu zaman kansu aiki ba, haka nan ba mu ga wata Ramadan ba. Don haka, muna mamakin yadda aka dangana mana kuɗaɗen Azumin Ramadan da kuma kyautar Idin Sallah.
“A matsayinmu na gwamnati, mun himmatu wajen tabbatar da gaskiya a dukkan ayyukanmu na mulki. Mun yi wa al’ummar Jihar Zamfara alƙawarin kawo sauyi mai kyau, kuma mun ƙuduri aniyar cika wannan alƙawari. Aikin ceton gwamnatinmu cikakke ne kuma ya shafi dukkan vangarorin mulki. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba ko kuma a rage mu da wani mummunan labari.”
