An kashe wata mata saboda mafarki a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An gurfanar da wasu maza su biyar kan zarginsu da yin taron dangi wajen kashe wata mata saboda mafarkin da wata ta ba su labari a Jihar Kano.

Kotun Jihar Kano mai lamba 14 da ke zamanta a titin Miller ta gurfanar da su ne kan zargin haɗa baki da kashe matar saboda zarginta da maita.

Mai gabatar da ƙara, lauyan gwamnati, Barista Lamido Abba Soronɗinki ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin su biyar suka haɗu suka kashe wata mata mai suna Ɗahara Abubakar.

Barista Lamido Abba Soronɗinki ya ce a garin Daɗin Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Wudil sakamakon ne wata mata mara lafiya da ta bayyana cewa ta yi mafarki cewa marigayiyar ta biyo ta da wuƙa.

Hakan ya sa waɗanda aka gurfanar suka dogara da mafarkin nata har suka yi wa marigayiya Malama Ɗahara Abubakar wannan ɗanyen aikin.

Dukkanin waɗanda ake zargin sun musanta laifukan da ake zarginsu na haɗin baki wajen aikata kisa da suka saɓa da Sashe na 97 da 221 na Kundin Pinal Kod.

By Editor