Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kungiyar Kamfanin Tsaro Masu Lasisi Masu Zaman Kansu na Nijeriya, reshen Jihar Kano ta zabi sabbin shugabanni a zaben da aka gudanar a harabar hukumar jami’an tsaro masu kulada fararen hula na jihar Kano.
An yayin zaben an zabi Dakta Idris Adamu Pukuma shugaban kamfanin tsaro na Pama Global Security a matsayin shugaban kungiyar ba tare da hamayya ba, sannan an zavi Alhassan Bello Samsam a matsayin mataimakin shugaba da Mista.Williams Michael na kamfanin tsaro na “Original Security “a matsayin sakatare janar na kungiyar da sauran wadanda aka zaba a mukamai daban-daban na kungiyar.
Da yake jawabi bayan zaben sabon zababben shugaban kungiyar Dakta Idris Adamu Pukuma ya godewa mambobin kungiyar bisa goyon baya da suka ba shi da hadin na zaben da suka yi masa a mukamin ba tare da hamayya ba.
Ya yi alkawarin ba da fifiko don hadin kai a tsakanin yan kungiyar da bunkasa cigabanta, sannan ya bukaci membobin da su kasance masu hakuri da juna domin harkar tsaro shi ne mafi muhimmanci ga kowa, kuma kowa ya kasance akan yin aiki tukuru don ganin daukakar kungiyar zuwa gaba.
Ya ba da tabbacin cewa za su yi komai tare da dukkan manyan shugabannin zartarwar kungiyar don ganin kungiyar ta sami cigaba da bunkasa tare da gudanar da ayyukansu daidai da tanadin doka.
Shugaban kungiyar kwararrun kamfanonin tsaro masu lasisi na Jihar Kano. Dokta Idris Pukuma ya ce irin kamfanoninsu suna da kwarewa na tsaro suna bada gudunmuwa wajen bada tsaro daga tushe suna bada tsaro ga kadarorin gwamnati, kamfanoni, kungiyoyi masu zaman kansu da ofisoshi da gidajen daidaikun jama’a.
Ya kara da cewa, irin kamfanoninsu na tsaro su ne mafi girma wajen da samar da ayyukan yi a Nijeriya da ma duniya domin ko’ina ana bukatar tsaro.
Ya ce, harkar tsaro ba wai kawai mutum ya je ya sami rijistar yin kamfani bane, idan mutum ya yi haka yana aiki ba bisa ka’ida ba kuma vata gari ne. Dole ne sai mutum ya nemi sahalewar hukuma karkashin ofishin ministan harkokin cikin gida bayan an tantance shi sannan hukumomin tsaro daban-daban sun tantance su sannan za a basu izini na doka.
Ya yi nuni da cewa, yanzu lamarin tsaro a kasar nan ya zama wani abu mai tsanani, ba abu ne da za ka iya daukar wani mutum daya a matsayin maigadi ba, yakamata ka sami kwararre, ne a kan tsaro waxanda ke da ilimi mai zurfi a harkokin tsaro da ke aiki bisa doka.
Dr. Idris Adamu Pukuma ya ce daga cikin kalubalen da kamfanonin tsaro masu zaman kansu ke fuskanta a Jihar Kano a yanzu akwai rashin basu haxin kai daga daidaikun mutane, wasu ba su san muhimmancin daukar kwararrun kamfanonin tsaro ba, idan ka dauki kamfanin tsaro za ka samu karancin matsaloli saboda kwararre zai kula da duk matsalolin tsaro yanda yakamata. Pukuma ya tabbatar da cewa da yardar Allah a cikin shekara mai zuwa za su shirya gangamin wayar da kan jama’a don sanar da su mahimmancin daukar kamfanonin tsaro masu zaman kansu don magance m
