Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Na samu halartar wani taron kaddamar da littafin da wata matashiyar marubuciya ta wallafa da harshen Turanci, mai suna Shackles of Abuse, wato Sarkakiyar Cin Zarafi, labarin bautar da ’ya’ya mata cikin lalata. Ko da yake ba ina son yin sharhi kan littafin ba ne, sai dai labarin da jigon littafin ya tavo ne ya tava zuciyata, kuma na ga ya dace mu yi nazari a kansa cikin wannan mako.
Labaran da ke cikin wannan littafin suna da tsoratarwa da firgitarwa ainun, musamman irin yadda marubuciyar ta rika kwatanta halin da ta samu kanta a ciki da wasu yaran mata irinta, sakamakon rashin imani da rashin tausayin da wasu ’yan uwa na jini suka riqa nunawa a rayuwarsu, da kuma tursasa musu shiga mummunar rayuwa.
Littafin ya dubi halin kunci da bakin ciki ne da wasu yara mata kan shiga sakamakon irin yadda wasu makusantansu, da suka hada da uba, kanin uba, ko kanin uwa, wa, abokin wa, da makamantan su ke jefa rayuwar su cikin wani hali na cin zarafi ko dai ta hanyar fyade ko yin lalata da su ta hanyar tsoratarwa ko amfani da karfi ko jan ra’ayinsu ta hanyar yaudara, da ke vata musu tarbiyya da rayuwa baki daya.
Ba bakon labari ba ne a ji cewa, wani uba ya yi wa ‘yar sa ciki, ya yi lalata da ita ko ya yi wa wata karamar yarinya cikin ’ya’yansa ko na makwafta fyade. Ko kuma a samu wani dan uwa na jini da aka amince masa a cikin gida yana lalata da wata daga cikin ’ya’ya mata na gidan ko ‘ya’yan ‘yar uwarsa ko dan uwansa. Wannan cin amana da cin mutuncin dan Adam da ake yi wa ’yan mata da kananan yara cikin yanayin da ake ganin akwai yarda da aminci, babban abin damuwa ne, ba kawai ga yaran da ake yi wa wannan cin zarafi ba har ma da iyayen yaran, musamman mata.
Ana sanya firgici, tsoro da rashin yarda a zukatan yaran da suke girma da tunanin duk wani namiji ko makusancinsu ba abin yarda ba ne, mugu ne ko azzalumi ne da ke shirin cutar da su da lalata makomarsu.
Akasari masu aikata irin wannan mummunar halayya ba a cika hukunta su ko gurfanar da su gaban hukuma ba, saboda ana ganin matsala ce ta cikin gida bai kamata a tona asirin abin da ya faru ba, don kada a vata sunan yarinya ko wanda ya aikata mata wannan mummunar aika-aika. Don haka ba sa sanin illar abin da suka aikata da hadarin sa ga tunani ko dabi’unta da mu’amalarta da sauran maza na cikin gida da na waje.
Wani lokaci a kan samu kuskuren hadin bakin uwa ko sakaci da kawar da kanta, idan ya yi yawa, ga mu’amalar da ke faruwa tsakanin uba da ‘yar sa, ko kanin uwa da ‘yar ta, da sauran irin wannan alaka, ba tare da ta yi bincike ko tsawatarwa kan wasu abubuwan da ta gani yana faruwa a tsakanin su ba. Tana ganin kamar yarda ce, haduwar jini ne ko zumunci ne. Alhalin tana iya yiwuwa abin da shi wannan uba ko dan uwa yake yi wa wannan yarinya a cikin daki ko a boye ba abu ne mai kyau ba, kuma ya saba wa tarbiyya ta al’ada da addini.
Wasu yaran suna tsoron bayyana abin da ke faruwa a tsakanin su da makusantan su ne, saboda tunanin ba za a yarda da su ba, ko za a zarge su da yi musu sharri ko bata suna. Ko kuma idan wadannan mazajen sun yi musu wata barazanar kisa ko yaudarar za su basu kudi ko wani abin duniya da yaran ke kwadayin samu.
Don haka sai su yi gum da bakin su, abin na ta faruwa a boye, har sai Allah ya tona asirin su. Kafin a farga da wuri tuni barnar da ake gudu ta auku. An koyawa yarinya lalata da maza, ko an nuna mata wata rayuwar da bai kamata a shekarun da take ta sani ba.
A irin wannan yanayi, wadanda ake bai wa ko ya kamata su rike amanar tarbiyyarsu ne suke cin wannan amana, su ne suke sauya rayuwar yaransu da kansu. A karshe a ga yarinya tana yin wani abu da ya sabawa hankali da tarbiyya har a shiga dora wa wasu da sunan makiya ko aljannu, domin yadda abin ya fara tava mata kwakwalwa ko ya jirkita mu’amalarta ta da ta sauran jama’a.
Babu wata kididdiga a hukumance da ake da ita na adadin yawan yaran da ake lalatawa rayuwa ko wadanda ake yaudara a jefa rayuwar su cikin kuncin rashin kyakkyawar makoma, da zubewar darajar kai. Saboda yadda yaran da iyayensu ke kunyar bayyana abin da ya faru da kuma boyewa saboda gudun vata sunan wanda ya aikata varnar. Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi hasashen a cikin yara 10 shida daga cikin su an taba yi musu fyade ko wani nau’i na cin zarafi yayin da suke gaban iyayensu ko hannun wasu makusantan su.
Ana samun cin zarafi ko cin amanar tarbiyya da raino a kowacce irin al’umma, kabila ko addini. A tsakanin ’yan kauye gidadawa ko wayayyu ’yan boko. A kasashen Turawa, Larabawa, ko bakakenmu na Afirka. Sai dai an gano cewa fiye da kashi 95 cikin dari na irin wadannan munanan halaye za a iya kaucewa faruwar su da magance su ba tare da sun yi illa ba, amma sakaci da rashin kula ko nuna damuwa shi yake kara munana abin.
Fiye da kashi 50 cikin dari na cin zarafin da ake yi wa kananan yara daga makusantan su ne wadanda su ma suke da nauyin tarbiyyar yaran a kansu. Yayin da ake cewa kimanin kashi 25 cikin dari na yara masu alamun shiga shekarun balaga daga 12 zuwa 17 da ake samun rahoton an ci zarafin su na kusa da su ne yake fara sa su cikin wannan rayuwar.
Ba ’ya’ya mata kadai ake yi wa cin zarafi ba, har da maza. Sai dai kididdiga na nuna cewa, an fi cin zarafin yara mata fiye da maza, duk kuwa da kasancewar ba a cika kai hankali ko sa ido a kan nasu bangaren ba. Suleiman wani yaro ne mai kimanin shekaru 12, wanda wata bazawara kanwar mahaifinsa ta rika koyawa lalata tana kwanciya da shi ba tare da sanin kowa ba, har kuma hakan ya yi tasiri a rayuwar sa wajen mu’amalarsa da sauran mata da ya rika hulda da su bayan ya girma.
Yara maza da mata da aka bude musu ido da jima’i ko hanyoyin saduwa tsakanin mace da namiji, ko tsakanin jinsi guda, suna fuskantar wata matsala ta kwalwalwa inda suke girma cikin wata kazamar rayuwa da kullum suke nadama da takaicinta. Za su rika aikata wasu abubuwa na fasikanci, ko bin maza, ko mata barkatai ba tare da suna samun wani jin dadi daga abin da suke aikatawa ba. Wanda hakan ke cutar da lafiyar tunaninsu, da zamantakewar su da mutane.
A makon da ya gabata, Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da wani tsari na kakkabe batagari da ke aikata munanan laifuka da ayyukan rashin tarbiyya a dukkan fadin jihar, inda daga ciki ya hada da rufe gidajen rawar Gala da gidajen karuwai, saboda kasancewarsu mafakar barayi da ’yan fashi. Abin takaici daga cikin matan da aka kama har da kananan yara da ba su wuce shekaru goma sha biyu zuwa sha biyar ba. Wasu ma an same su da ciki, wasu da kananan goyo. Duk kuma wadannan abubuwan na da nasaba da muhallin da yaran suka tashi da abubuwan da wasu maciya amana da makusanta suka koya musu ne.
Lallai ne iyaye su zama masu kula da sa’ido kan irin shakuwa da yaransu kan yi da wasu manya makusanta, ko wadanda ba su aminta da halayensu ba. Sannan su kula da irin ’yan’uwan da wadannan yara ke tsoron zuwa kusa da su, saboda mai yiwuwa akwai abin da suke yi musu marar kyau da yaran basa jin dadinsa.
Ko wata barazana da suke yi musu, don su tsorata yaran su amince musu. Ita ma kuma gwamnati ta fahimci cewa, sanya irin wadannan yara a cibiyoyin gyaran tarbiyya zai taimaka musu wajen canja halayensu da harkokin su na rayuwa.
