Mutane za su ƙara shiga wahala a wasu yankunan Arewacin Nijeriya – Bankin Duniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Bankin Duniya ya yi hasashen za a ci gaba da samun tabarbarewar matsalar tsaro da rikicin ‘yan bindiga da matsin rayuwa a kananan hukumomin jihohin Borno da Kaduna da Katsina da Sakkwato da Yobe da Zamfara da kuma Adamawa har zuwa watan Mayun 2024.

Hasashen bankin na zuwa ne daidai lokacin da ya bayyana cewa rashin nagartattun tsare-tsaren tattalin arziki sun haifar da raguwar samun amfanin gona a Nijeriya.

Wannan dai zai shafi batun samar da hatsi a kasar. Bankin Duniyar ya bayyana haka ne a rahoton baya-bayan nan da ya fitar game da samun wadataccen abinci.

Kiyasin hatsin da ake sa ran nomawa a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya a bana ya kai sama da tan miliyan 76, an samu ragin kashi biyu cikin 100 daga kakar da ta gabata, sai dai an samu karin kashi uku cikin 100 na matsakaicin adadin a cikin shekara biyar.

Ana sa ran koma-bayan zai fi tasiri ne a kasashen Chadi da Mali da Nijar da kuma Nijeriya.

A rahoton na baya-bayan nan, bankin duniyar ya ce a tsakanin watan Agusta da Nuwamba, kasashe da dama marasa karfin tattalin arziki sun yi fama da hauhawar farashi.

By Editor