2024: Gwamna Lawal ya rattaba hannu kan kasafin  N426bn

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A ranar Asabar da ta gabata Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannun kan kasafin shekarar 2024 na Naira biliyan 426.

Kasafin wanda aka yi wa take da “Kasafin Ceto”, ya samu amincewar Majalisar Dokokin Jihar ne a ranar Juma’ar da ta gabata, inda washegari Gwamnan ya rattaba hannu ya zama doka.

Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a sanarwa da ya fitar cewa, daga cikin N426,563,671,000.00 da aka amince da shi a matsayin kasafin 2024, an ware wa ayyukan yau da kullum N118,358,079,515.00, yayin da aka ware wa muhimman ayyuka N308,205,591,485.00.

Ya kara da cewa, kasafin zai bunkasa sha’anin zuba jari a gida da waje da kuma bunkasa harkokin kasuwanci a fadin Jihar Zamfara.

A cewar sanarwa, “Kasafin 2024 da Gwamna sanya wa hannu zai ba da fifiko ga muhimman bangarori guda shida don cigaban Jihar Zamfara; bangarorin sun hada da tsaro, ilimi, harkar noma, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da sauransu.”

Kazalika, sanarwar ta nuna cewa, an ware wa bangaren gudanarwa – N72,093,326,763, tattalin arziki – N244,729,584,729, kyautata rayuwa – N103,139,659,508, bangaren shari’a – N6,601,100,000.”

Sauran sun hada da; harkar noma – N38,144,000,000; ilimi – N51,370,787,508; kiwon lafiya – N33,922,370,000; sai kuma bangaren samar da ababen more rayuwa da bunkasa birane da ya tsira da biliyan N109.

By Editor