ACF za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta zaman lafiya – Ƙungiyar Matasan Arewa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Kungiyar Tuntuva ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa kungiyar ta shirya tsaf domin samar da zaman lafiya, hadin kai da samar da wadata a fadin Arewacin Nijeriya baki daya bisa ingantaccen tsari.

Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin matasan Arewa (JACOM), sun yi amanna da kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) domin ganin an samu sauyi tare da sauya akalar shugabancin kungiyar ta fannin zamantakewa da al’adun Arewacin Nijeriya.

Kungiyar Matasan Arewa, a wata sanarwa da Murtala Abubakar, shugaban JACOM da Israel Musa, Sakatarenta suka fitar ya bayyana cewa ci gaban da kungiyar ta ACF ta yi ya kan kama ns a makon da ya gabata yayin kaddamar da sabon kwamitin zartarwa na kasa don gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa bayan karewar wa’adin tsohon ministan noma, Dattijo Audu Ogbe.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “sauyin da aka samu cikin kwanciyar hankali da lumana ya biyo bayan yunkurin da kwamitin zabe wanda ya samar da kungiyar zartaswa a halin yanzu a karkashin jagorancin Mamman Mike Osman SAN, shaida ce a sarari ga jajircewar ACF na tunkarar nauyin da ke kanta da sabbin dabaru da fa’idoji.”

“Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin matasan Arewa yana da yakinin cewa bin bayanan mutanen da suka kafa sabuwar kungiyar zartaswa da aka kaddamar, da manufar kafa kungiyar ACF da dai sauransu, don samar da zaman lafiya da hadin kai da samar da cigaba a fadin kasa bakidaya.”

“A yayin da muke sa ido kan manufofin shugabanci na yankin Arewa a halin yanzu, kungiyarmu ta tabbatar wa ACF cikakken jajircewarmu da daukacin al’ummar Arewacin kasar nan a shirye muke mu hada kai da sabon kwamitin zartarwa na ACF ba wai don tabbatar da hadin kai ba kawai, amma sai don kara wa matasa kuzari da hikimar don tunkarar kalubale, sannna kuma don dawo da tsaro, zaman lafiya, hadin kai da cigaba a yankinmu don fatan alheri da kuma don gobe, musamman a wannan mawuyacin lokaci”, inji sanarwar.

Sanarwar ta ce, “muna kira ga daukacin ‘yan Arewa ba tare da la’akari da harshe, addini, tsatson ko siyasa ba da su hada kai su baiwa ACF goyon bayan da take bukata domin sauke nauyin da ke kanta.”

By Editor