Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamnonin Filato, Ebonyi

Spread the love

A ranar Juma’a Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara na soke nasarar da Gwamna Caleb Mutfwang na Jam’iyyar PDP ya samu a zaben 2023.

Kotun Kolin ta ce kotun farko ta yanke hukunci a kan abin da ba shi da hurumin kotu ta saurare shi.

Don haka Kotun a karkashin jagorancin Mai Shari’a Emmanuel Agim, ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe wanda ta ayyana Mutfwang a matsayin zababben Gwamnan Filato.

Alkalin ya ce Muftwang ya cancanci tsayawa takara saboda sahihin zaben fidda gwani aka yi kafin ya samu tsayawa takarar gwamna.

Kotun ta ce Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ba ta da hurumin sauraren korafin da aka yi na tsayar da Mutfwang takara. Haka nan, cewa a matsayin APC ba mamba ba ce a PDP, ba ta damar kalubalantar PDP kan yadda aka yi ta samu dan takararta.

A wata mai kama da wannan, Kotun Koli ta yanke hukunci kan cewa Francis Nwifuru shi ne zababbenn Gwamman Jihar Ebonyi.

Mai Shari’a  Tijjani Abubakar, shi ne ya yanke wannan hukuncin a ranar Juma’a, inda ya yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta, Chukwuma Odii suka daukaka na kalubalantar nasarar da Nwifuru ya samu a zaben 2023.

By Editor