Gwamna  Abba ya kammala shirye-shiryen kafa Majalisar Dattawan Kano

Spread the love

*Ganduje, Kwankwaso, Shekarau za su kasance mambobin farko

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta kammala shirin kafa Majalisar Dattawan Kano a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne sa’ilin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Abuja, inda ya ce Majalisar za ta kasance a mazaunin mai bai wa gwamnatin jihar shawarwari wadda za ta kunshi tsofoffin gwamnoni da mataimakansu.

Abba ya ce bayan kafa majalisar, dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dokt Abdullah Umar Ganduje da tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau da sauransu, su za su zama mambobi na farko na majalisar.

Gwamnan ya jaddada aniyarsa ta gudanar da mulki kofarsa a bude domin kowa ya shigo a tafi tare don cigaban Kano.

Sai dai babu cikakken bayani kan ko tsoffin shugabannin za su amince kowa ya ajiye bambancinsa a gefe guda sannan a hadu a yi aiki tare don cigaban Kano.

By Editor