AKCOE da FUDMA sun ilimantar da ɗalibansu yadda ake karatun digiri

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

A ranar Asabar da ta gabata ne shugabnnin hukumar kwalegin ilimi ta Aminu Kano, mai hadin gwiwa da Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsin-ma tare da sauran fitattun masana da shugabanni a matakin jiha da na tarayya da sarakuna da sauran al’umma suka taru a harabar kwalejin AKCOE dake Kano wato Aminu Kano College of Education.

Domin taron wayar da kan dinbin dalibai da suka samu shiga wannan kwaleji domin karatun digiri a kwalejin inda masana da dama karkashin shugabancin shugaban hukumar zartarwa na kwalejin Farfesa Tijjani Hassan Darma, da sauran masana suka gabatar da jawabai na ka’idoji da kuma yadda zaman karatun digiri ya banbanta da yadda ake karatun sakandire da sauran makarantu nag aba da sakandire.

Wanda ake samun shedar NCE ko Diploma a wadanan makarantu na baya domun shi karatun digiri abu ne da aka tsara na cewa wanda ya karanta digiri to ko wanne nauyi na shugabanci da gudanarwa zai iya hawa kansa a ko ina a Nijeriya da wajenta dan haka zaman karatun yin digiri ya sha ban ban da sauran matakan karatu a Nijeriya.

A jawabinsa, Shugaban Kwalejin ta AKCOE na yanzu, Dr Ayuba Ahmad Muhammad, ya bayana cewa yadda suke samun hadin kai daga wannan jami’a ta Faduma, da kuma gwamnatin kano wani abun alfahari ne a wannan lokacin musammam ganin yadda ita gwamnatin kano ta wannan lokaci ta ba ilimi mahinmanci musammam yadda take daukar nauyin dalibai zuwa kasashen waje domun karo karatu a matakin digiri na biyu.

Wannan abun a yabawa gwamnatin ne kuma wannan ce tasa wasu daga cikin kwamishinoni na gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke bugar kirji wajen biyawa wasu dalibai kudin makaranta a kashin kansu wannan kuma baya rasa alaka da yadda ita kanta gwamnatin kano ta zaftare kudin makaranta na kashi 50 cikin 100 a makarantun gwamnatin kano nag aba da sakandire da kuma biyawa daliban jami’a sama da 7,000 kudin makaranta a kokarin gwamnatin na bunqasa ilimi a jahar kano, dai dai da manufar kafa kwalejin AKCOE na bada ilimi maiinganci a tsakanin al’uma baki daya.

A karshe Dr Ayuba, ya yi kira ga daukacin daliban da Allah ya basu dama nayin wannan karatu na digiri da su mai da hankali wajen ganin basuyi wani abu da ya sava tarbiya da ka’idojin makaranta ba musammam kasancewarsu matasa manyan gobe wanda Kano da Najeriya, dama duniya baki daya zatayi alfahari da su musammam in suka zama masu nagarta da nutsuwa ta hanyar kaucewa miyagun kungiyoyi da shan miyagun  gwayoyi da hukumomi ke yaki da dukanin masha’a a Nijeriya.

By Editor