‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 17, sun kashe ɗaya a Katsina

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD

Wasu gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki garin Burdugau da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 17 tare da kashe mutum ɗaya.

Wakilinmu ya rawaito cewa, yayin farmakin ‘yan bindigan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren Lahadi inda suka shiga gida-gida.

Majiya ta ce ‘Sun yi awon gaba da ɗaruruwan dabbobin da suka haɗa da awaki, tumaki, shanu, sun yi garkuwa da mata sama da 17, musamman matan aure da wasu ‘yan mata, sun kashe mutum ɗaya da aka fi sani da suna Uban Sabga.

“Yawancin waɗanda aka sace matan aure ne da kuma ‘yan mata kuma mun binne wanɗanda aka kashe da sanyin safiyar yau,” in ji majiyar.

Majiyar ta ƙara da cewa, “Ina so in yi amfani da wannan damar domin yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Katsina da su kawo mana ɗauki cikin gaggawa.”

Wakilinmu ya ce ‘yan ta’addan sun fasa shaguna da dama na ‘yan kasuwa tare da sace kayan abinci a yayin harin.

Ya kuma ƙara da cewa kashi 80 na mazauna yankin sun bar yankin ne saboda fargabar sake aukuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

By Editor