Daga BASHIR
A halin da ake ciki, haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya zanaga-zangar lumana a sassan ƙasa domin nuna rashin jin daɗinta game da ƙuncin rayuwar da ‘yan ƙasa ke fuskanta.
Bayanan da MANHAJA ta kalato a ranar Talata sun nuna an hangi masu zanga-zangar a yankin Ikeja, Jihar Legas.
Inda aka ga da damansu ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar “A kawo ƙarshen yunwa da talauci yanzu” da dai sauransu.
A Jos babban birnin Filato ma haka lamarin yake, a nan ma an ga ɗaruruwan masu zanga-zangar sun mamaye wasu manyan hanyoyin birnin.
Haka ma a jihohin Bayelsa da Abuja da sauransu, duk ba ta sake zani ba.
Ƙungiyoyi daban-daban ne suka shiga zanga-zangar domin nuna nuna rashin jin daɗinsu dangane da tsadar rayuwar da ‘yan Nijeriya ke fama da ita.
A baya, NLC ta fitar da sanarwa inda ta ayyana ranakun 27 da 28 ga Fabrairun 2024, a matsayin ranakun da za ta gudanar da zanga-zanga ta lumana domin jawo hankalin gwamnati zuwa ga aikata abin da take ganin shi ne mafita game da halin da ƙasa ke ciki.
