Darasin haƙuri a zamantakewa (3)

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanku da jimirin karatun Manhaja. A mako da ya gabata mun fara kawo muku da bayanai a game da yadda za a gyara aure ta hanyar yin haƙuri a gidan Malam Bahaushe. Amma fa haƙurin ta ɓangaren masu gida, wato maza.

A makon da ya gabata mun fara kawo muku wasu bayanai game da yadda su maza suke ganin su yin haƙuri a zamantakewa ta aure bai kama su ba. Kuma al’umma duk suna neman su amince da haka. Amma a zahirin gaskiya ta fuskar zamantakewa da addini ma ya kamata a ce kowanne ɗan Adam yana yin haƙuri a harkar zamantakewa da rayuwar duniya. Allah (SWT) a littafinsa mai tsarki ya faɗa mana fa’idojin haƙuri birjik. Haka ma Annabin rahama Sallallahu alaihi Wasallama.

A makon da ya gabata mun fara kwararo muku bayani a kan illolin raahin haƙurin maza a zamantakewa. A wannan makon kuma za mu zo muku da maslaha a kan rikicin da hakan ke kawowa. A sha karatu lafiya.

Hanyoyin da za a bi a kiyaye rikici sun haɗa da, idan saɓani ya afku a gidan aure, kawai sai wanda ya san shi ne da laifi ya fito ya amsa laifin ya ba da haƙuri. Ba kuma wai ba da haƙuri kawai ba, a ba da haƙuri da zuciya guda. Ba wai ka ce na san laifina ne amma kaza-da-kaza. A’a ba da haƙuri kawai. Idan macen ce ma haka. Za mu tsaya a nan sai mako na gaba za mu ci gaba idan rai ya kai. Jinjina da godiya ga masu kira da addu’a da fatan alkhairi. Allah ya ƙara albarkar rayuwa kuma ya biya dukkan muradai.

An san dai da matuƙar wahala hakan. Musamman ma a wajen maza. Suna ganin kamar zub da girma ne ko ja wa kai raini ne ya nuna ya amshi laifinsa. Amma zai samu kwanciyar hankali. Shi girman kai rawanin tsiya ne. Sam ba shi da riba sai asara. Ma’aurata ku sauke girman kai. Ko don kwanciyar hankalin yaran da suke tsakaninsu.

Ita da ma mace a shar’ance ita ce a ƙasa. Shi kuma namiji shi ma ya ajje girman nasa ya amsa laifinsa. Ya daina ganin zaman aure a matsayin alfarma ga mace. Sai auren ya mutu kuma, sai ya gane shayi ruwa ne. Wani ma sai bayan guri ya ƙure masa zai gane illar rabuwa da mace mai yara. Gabaɗaya hankalinsa da nata ba zai ƙara kwanciya ba. Ko da ta yi wani auren ko shi ya yi wani auren.

Kullum yana tunanin yadda ake riƙe masa yara. Ya qi ha quri da uwarsu ga shi kuma dole ya yi haƙuri da wata, ba yadda zai yi. Ita ma idan ya saka, bai sn wacce zai jajibo ba. Wani mafarin aure-aurensa kenan. Ko da ba shi da ra’ayin tara mata.

Don haka, dole a ƙara haƙuri da abokiyar zama. Mace ce fa. Kuma shekarunsa mai yiwuwa sun ninka nata. Ga hankalinsa ba irin nata ba. Don haka dole ka yi uzuri mai tsaho. Sannan kuma dole ya koyi yafiya mai yawa. Idan ba haka ba, ya biye wa shawarwarin sakin ta ko ƙaro mata kishiya, kwavarsa za ta yi ruwa.

Kuma ba qarin auren aka ce babu kyau ba. Amma ka ƙaro aure don Allah (SWT), don raya sunnar Manzon Allah (SAW). Ba wai don kana son ka rama abinda matarka take maka ba. Ko kuma don kana so ka gyara halinta ba. Haka rabuwa idan ta zo, a rabu saboda ita ce maslaha.

Ba wai don ka hukunta matarka a kan laifin da ta yi maka ba. Wannan babban kuskure ne. Eh an san idan an yi rabuwar aure mace da iyayenta a lokacin da abun ya faru, sun fi tagayyara musamman ma idan da yara a tsakani. Amma fa shi ma namijin yana ɗanɗana tasa kuɗar duk da dai shi sai a gaba zai fuskanci shi ma abin ya shafe shi, matuƙa

Sannan kuma ya kamata idan saɓani ya faru a tattauna matsalar a wuce wajen. Kada a ce za a yi gaba ko a ƙullaci juna. Ko kuma a ce wai sai an yi ramuwar gayya wacce Hausawa kan ce ta gi ta farau zafi. Irin dai yadda abokan gaba suke yi min kan kara, na yi maka na itace. Kuma su sani, gaba da riƙon juna ba ƙaramar illa yake kawowa ba a zaman aure. Gaba tana ƙara sawa a nesanta da juna. Kuma rashin fahimta ta ƙara tsananta a gidan auren. Har wani lokacin ma ya kawo rabuwa.

Idan an samu rashin jituwa a tsakanin ma’aurata, ya kamata bayan sun sakko, fushi ya ɗan ragu, to a zauna a tattauna matsalar. Barin matsaloli su taru a tsakaninsu shi ne a ma fi yawan lokuta yake rusa aure. Ba a tsaya an fuakanci juna ba.

Kowa ya ƙullaci abokin zamansa. Kuma ƙullatar abokin rayuwa a zuciyarka shi yake sawa soyayya da kyautatawa gare su ita ma ta ragu. Idan abu ya wuce, kawai ya wuce. A yafe wa juna kuma a kiyaye gaba. Hakan shi ya kamata, ba wai rabuwa ba.

Sannan kuma kada namiji ya dinga ɗauka kullum shi ne a dai-dai. Ya kamata a ce idan matsala tana yawan faruwa da iyalinsa, ya zauna ya yi karatun ta-nutsu ya ga anya shi ma ba shi da wani hali da yake buƙatar ya gyara? Idan ya gano, sai ya gyara a zauna lafiya.

Idan tunaninsa bai iya ba shi amsa ba, zai iya tamabayar matar ya ji ta bakinta. Cikin dabara suna raha, ya ji wai shin daga cikin halayensa wanne ne yake ci mata tuwa a ƙwarya? Za ta iya sakin jiki ta gaya masa. Shi kuma zai amfani da hikima wajen ganin ya gyara.

Bayan haka kuma ma’aurata su sani, aure fa ibada ne ba wai gidan varje gumi ba. Ibada kuma ba ra’ayi ce ba. Bin umarnin Allah ne, tsantsa ba son rai ba. Haka kuma dole idan za a gina alaƙa mai ɗorewa, ana buƙatar sadaukarwa. Dole sai an haƙura da wani jin daɗin sannan a gina rayuwa mai kyau. Sannan a sama wa zuriyya makoma mai kyau.

Su ma mata a nasu ɓangaren, ya kamata su zama masu haƙuri da biyayya. Ki guji tunzura miji ta hanyar ramuwar gayya a kan dukkan abinda ya yi miki. Idan laifi ne ki zauna ku sasanta. Idan sasancin bai yiwu ba, ki zamo mai yawan yafiya da uzuri. Ki guji yi masa abinda zai tura shi ya sake ki. Ki dinga tunawa da makomar ‘ya’yanki.

Sannan ki tuna a cikin al’ummar da kike. Wacce take ganin laifin bazawara amma ba ta ganin laifin wanda ya yi sakin. Sannan kuma ki tuna sai kin fi tagayyara fiye da mijinki. To me ya yi zafi? Ki kama kanki, ki zauna lafiya da mijinki kamar yadda Allah ya shar’anta. Sai mako na gaba idan Allah ya mana tsahon rai.