Rayuwar Sarki Haile Selassie na Habasha

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Haile Selassie an haifeshi a ranar 23 ga watan Yuli na shekara ta 1892 a kusa da Harar cikin ƙasar Habasha, inda aka raɗa masa suna da Tafari Makonnen. Mahaifinsa amintacce ne kuma na kusa da Sarki Menelik na II. An kira shi zuwa kotu a Addis Ababa lokacin da babansa ya mutu a 1906.

A 1916 ya zama mabiyin aqidar Ras Tafari, da ake zaton ya gaji sarauniya Zauditu da ke zaman ‘ya ga Menelik na II. A shekara ta 1928 tare da magoya bayansa sun sanya sarauniyar ta ba shi sarauta.

A shekara ta 1930, bayan mutuwar sarauniya Zauditu an naɗa Tafari a matsayin sarki. An riƙa kiransa Haile Selassie, ma’ana”Babban mai aika saƙo”. An masa juyin mulki ƙarƙashin jagorancin sojoji masu goyon bayan tsarin Kwaminisanci a shekara ta 1974, ya kuma rasu a ranar 26 ga watan Agusta na shekara ta 1975 a birnin Addis Ababa.

Ya gabatar da Kundin Tsarin Mulki na farko a Habasha a shekarar 1931, wanda ke tafiya da tsarin majalisa da ɓangaren doka, ya kuma nuna cewa dukkannin al’ummar ƙasar ta Habasha daya suke. Sai dai kundin tsarin mulkin ƙasar na farko da wanda aka yi a shekarar 1955 sun sha suka bisa zargin ba da ƙarfin iko ga sarkin ƙasar kasancewar yana da ƙarfin iko da zai iya fatali da duk wani ƙudiri da majalisa ta cimma, sannan babu hurumi na kafa jam’iyyun siyasa.

Da fari dai Tafari Makonnen an kalle shi a matsayin mai tsare-tsare managarta, ana ganin yana da hannu wajen sauke Sarki Lij Ilyasu da Zauditu ta gada, wanda ya yi mulkin shekaru uku kacal. A matsayinsa na sarki mai iko Haile Selassie ya tura ɗalibai da dama zuwa ƙasashen waje domin karatu, daga baya waɗannan ɗalibai su suka yi sanadin sauke shi daga mulki saboda kukan da suke na rashin samar da sauye-sauye. An yi yunƙuri na yi masa juyin mulki a 1960, babbar barazana ga mulkinsa wanda daga ƙarshe sojoji masu goyon bayan tsarin kwaminisanci suka yi gaba da kujerarsa.

A matsayinsa na wanda yake jerin waɗanda za su iya sarauta, Tafari ya sanya Habasha a Majalisar Ɗinkin Duniya a shekara ta 1923, ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka ƙalilan da ke cin gashin kansu, a lokacin ƙasarsa ce kaɗai ta samu damar zama mamba.

A 1963 sarkin ya bijiro da taron farko na ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Afirka (OAU) wacce daga bisani ta zama ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). Ya taimaka wajen fara tsara ayyukanta kana ya zamo shugabanta na farko, inda aka kafa hedikwatarta a birnin Addis Ababa.

Ganin yadda yake neman haɗin kan ƙasa da ƙasa ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe daban-daban, a shekarar 1954 ya kasance shugaban wata qasar waje da ya fara ziyarar sabuwar gwamnatin Tarayyar Jamus, abin da ya sa ya samu gagarumar tarba da biki mai ƙayatarwa da ake wa duk wani babban bako da ya ziyarci Jamus tun bayan yaƙin duniya. Ya kasance a gaba wajen nuna sha’awarsa a fannoni na lafiya da aikin gona da masana’antu, wadanda ya yi burin gani a Habasha. Kasarsa ta zama kawa ga Jamus sannan Haile Salassie ya samu tarbar karramawa a birnin Bonn na Jamus, shekara guda kafin a kifar da gwamnatinsa.

Haile Selassie ya yi yunƙurin zamanantar da ƙasar ta hanyar sauye-sauye na siyasa da zamantakewa, ciki har da gabatar da kundin tsarin mulkin 1931, da rubutaccen tsarin mulkinsa na farko, da kuma kawar da bauta.

Ya jagoranci yunqurin kare ƙasar Habasha da bai yi nasara ba a lokacin yaƙin Italo da Habasha na biyu kuma ya shafe mafi yawan lokutan mulkin Italiya yana gudun hijira a Ingila. A shekara ta 1940 ya tafi ƙasar Sudan domin ya taimaka wajen tsara gwagwarmayar yaqi da ‘yan ta’adda a ƙasar Habasha, sannan ya koma ƙasarsa a shekarar 1941 bayan yakin gabashin Afrika. Ya rusa Tarayyar Habasha da Eritriya, wadda babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya kafa a shekarar 1950, sannan ya mayar da Eritrea cikin Habasha a matsayin ɗaya daga cikin lardunanta, yayin da yake fafutukar hana ballewa.

Ra’ayin Haile Selassie na duniya ya kai Habasha zama memba na Majalisar Dinkin Duniya. A shekarar 1963, ya jagoranci kafa ƙungiyar haɗin kan Afrika, wadda ita ce farkon ƙungiyar Tarayyar Afirka, kuma ya zama shugabanta na farko. A cikin shekarar 1974, an hamɓarar da shi a juyin mulkin soja daga mulkin Marxist–Leninist, Dergi.

An kashe Haile Selassie a ranar 27 ga Agusta 1975.