‘Za mu ci gaba da zanga-zanga’ — cewar NLC

*Ganawarsu da gwamnati ba ta haifar da ɗa mai ido ba

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta ce za ta ci gaba da zanga-zangarta tun da ba a cimma maslaha ba a taron da suka yi da Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin.

Ɓangarorin biyu sun gana ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da zummar lalubo bakin zare dangane da zanga-zangar da NLC ke kan gudanarwar domin nuna rashin jin daɗinta da halin tsadar rayuwar da ‘yan ƙasa ke fuskanta.

Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce “Za a ci gaba da zanga-zangar, kuma haƙƙi ne a kansu su tabbatar da cewa zanaga-zangar ta gudana a cikin lumana.”

Taron ya gudana ne ba tare da sahale wa ‘yan jarida shiga ba, kuma ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Mahalarta taron sun haɗa da Babban Lauyan Ƙasa, Lateef Fagbemi; Ministan Ƙwadago da na harkokin noma da na kuɗi da na kasafi da tsare-tsare da kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da sauransu.

Tun da fari, Gwamnati ta roƙi NLC da ta janye zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a ranakun 27 da 28 ga Fabrairu sannan a yi zaman sulhu, lamarin da NLC ɗin ta ce babu gudu babu ja da baya.

An ga yadda a ranar Talata wasu sassan ƙasa suka amsa gayyatar NLC suka fita zanga-zanga, musamman a yankunan Abuja, Filato Legas da sauransu.