Lawal zai gina garejin manyan motoci a sassan Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bayyana cewa zai gina wuraren hada-hadar motocin kasuwa a Zamfara a matsayin ɓangaren ƙudirinsa na raya birane a jihar.

Lawal ya furta hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar masu motocin haya ta NARTO da ta direbobin tankokin dakon fetur, PTD.

Cikin sanarwar da Kakakinsa Sulaiman Bala Idris ya fitar, Gwamna Lawal ya ce, “Na ba da umarnin a gina garejin manyan motoci guda biyu, ɗaya a hanyar Funtua zuwa Gusau gudan kuma a hanyar Sokoto zuwa Gusau.

“Ni na gayyato NARTO da PTD kan su zo su shiga kwamitin don samar da yankunan hada-hadar abubuwan hawa.

“Za mu yi bincike mai zurfi domin gano wuraren da suka fi dacewa a gina garejin manyan motocin.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Shugaban NARTO na Jihar Zamfara, Alhaji Mustapha Musa Sarkin Kagara, ya bai wa Lawal tabbacin samun goyon bayan mambobin ƙungiyoyin biyu don cimma nasara.

Ya ƙara da cewa, bayan kammalawa aikin zai samar wa mutum sama da 5000 aikin yi a jihar.

Taron wanda ya gudana a ranar Talata, a Fadar Gwamnatin Jihar, ya tattauna batutuwa da dama ciki har har da samar da wuraren hada-hadar motocin safa, tattalin abubuwan hawa a birnin Zamfara da sauransu.