NLC ta janye ci gaba da zanga-zangar gama-gari

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta dakatar da ci gaba da zanga-zangar gama-gari na yini biyun da ta shirya.

Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a cikin sanarwar bayan taron da ta fitar bayan taron Majalisar Zartarwar ƙungiyar, tana mai cewa zanga-zangar ranar farko ta haifar da cigaba mai ma’ana.

Don haka ta je ta janye ci gaba da zanga-zangar a rana ta biyu biyo bayan nasarar davta samu a ranar farko ta zanga-zangar.

Da fari NLC ta ƙeƙashe ƙasa inda ta ce babu gudu babu ja da baya game da zanga-zangar yini biyun da ta shirya duk da ɓangaren gwamnati ya rarrashe ta, amma daga bisani ƙungiyar ta ba da kai bori ya hau bayan tattaunawar da ɓangarorin biyu suka yi a ƙurarren lokaci a ranar Talata.

Tsada da ƙuncin rayuwar da ‘yan ƙasa ke fuskanta na daga manyan dalilan da suka NLC shirya zanga-zangar tata.

A halin da ake ciki, ‘yan Nijeriya na ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyakin masarufi lamarin da ya jefa rayuwar ‘yan ƙasa cikin ƙunci.