Za a yi taron wayar da kan ‘yan Kannywood kan sabbin dokokin Hukumar NCC – KSCB

Hukumar kare haƙƙin masu mallaka tare da yaki da satar fasaha ta kasa (NCC), ta nemi haɗa hannu da Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano domin wayar da kan abokan hulɗarsu kan sabbin dokokin hukumar da waɗanda aka yi wa gyara.

Da yake jawabi a yayin ganawar sa da manema labarai, Alh Sani Ahmad wanda shi ne mai kula da jihohin Kano, Katsina da Jigawa na Hukumar kula da haƙƙin masu mallaka tare da satar fasaha ta kasa ya ce, ya ziyarci Hukumar ta tace Fina-finan ne a domin neman goyan bayan su ta yadda za su haɗa hannu kan wayar da kan abokan hulɗarsu musamman masu sana’ar waka, marubuta da shirya fina-finan tare da masu fassara fina-finai daga wani harshe zuwa yaren Hausa kan sabbin tanade-tanade da sabuwar doka da Hukumar ta yi dangane da yadda za su gudanar da ayyukansu.

Ahmad ya kara da cewa, doka ta ba wa hukumar su damar lura da ayyukan masu wannan sana’a tare da hukunta su yayin da aka same su da laifin karya dokokinta.

Tunda farko a nasa jawabin, Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano, Alh. Abba El-mustapha ya gode wa jami’an Hukumar kula da haƙƙin masu mallaka tare da satar fasaha ta kasa dangane da girmama Hukumarsa da suka yi na kawo ziyara ta musamman domin ƙulla alaƙar aiki tare da kawo hanyar da za a ciyar da abokanan hulɗa hukumomin nasu gaba.

A ƙarshe, Abba El-Mustapha ya yi alƙawarin bai wa Hukumar cikakken haɗin kai tare da goyon baya ta yadda za a cimma nasarorin ayyukan da aka sa a gaba.