Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Nijeriya za ta tura tawaga Nijar

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Sanatocin Jihohin Arewacin Nijeriya ta ce za ta tura wakilanta jamhuriyyar Nijar, domin ganawa da shugabannin mulkin sojin ƙasar, kan yadda za a mayar da mulki ga farar hula.

Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne, bayan sanar da janye takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar da Mali da kuma Burkina Faso waɗanda sojoji ke jan ragamar mulkin su.

Kakakin ƙungiyar sanatocin, Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya ce ƙungiyar za ta tura tawagar ba tare da vata lokaci ba.

Janye takunkuman da ECOWAS ta yi zai sake buɗe harkokin cinikayya da zai taimaka wajen warware matsalar ƙarancin abinci da magunguna da sauƙaƙa al’amura ga ƙasashen na Nijeriya da Nijar da ke makwabtaka da juna.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wata ƙungiyar malaman Musulunci ta Nijeriyar ta yi kira da sojoji a Nijar da Mali da Burkina Faso da su koma cikin ƙungiyar ta ECOWAS.

By Editor