Gwamna Dauda Lawal ya karrama askarawa 20 a Zamfara

Spread the love

Gwamna Dauda Lawal yayi alƙawarin ɗaukar nauyin iyalan askarawan wanda suka rasa ransu a yayin yaƙi da ɓarayin daji.

Askarawa 20 ne aka karrama da lambobin girma saboda jajircewar su a ranar Alhamis a gidan Gwamnatin da ke Gusau.

A wani jawabi da mai magana da yawun Gwaman Sulaiman Bala Idris yayi, yace askarawan tabbas sun nuna bajinta sosai.

A cewar jawabin, askarawan na ƙarkashin Jagorancin Birgediya Janar Lawal Bature Muhammad.

“A ranar Alhamis, Gwamna Dauda Lawal ya karrama 20 daga cikin askarawan saboda jajircewa wajen yin aiki tuƙuru. Dukkan 20 din suna kan gaba gaba wajen yaƙi da ɓarayin dajin domin ganin zaman lafiya ya dawo jihar Zamfara”

A yayin jawabin nasa, Gwamna Dauda Lawal ya ƙara tabbatar da irin jajircewa da gwamnatin sa keyi wajen ganin askarawan sunyi aiki cikin yanayi mai dadi, ya kuma bada alƙawarin ɗaukar nauyin iyalan wanda suka rasa ransu.

“Ku ɗauka cewa baku wannan lambobin girma ya zama ya ƙara zaburar daku domin yin aiki tuƙuru a kan wanda kuke yi”

” Ba zamu iya biyan ku ba saboda yanayin aikin da kuke, sai dai mu zaburar daku”

“Ina ƙara jaddada muku da cewa muna da tsari a ƙasa domin iyalan askarawan da suka ransu a yayin aiki. Zamu dauki nauyin iyalan nasu da basu duk wata kula da ya dace”

Kwamandan Askarawan Birgediya Janar Lawal Bature ya ce, askarawan 20 an zabo su ne daga ƙananan hukumomin jihar Zamfaran.

Sulaiman Bala Idris
Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, 15 ga Yuni, 2024

By ukarofi