Wike zai tashi kasuwar ‘Mechanic Village’ zuwa Wassa

Spread the love

Daga KHADIJA ABUBAKAR

Majalisar kula da ayyukan birnin tarayya, AMMC ƙarƙashin ofishin ministan Abuja, Nyesom Wike, ta ce za ta sauya wa makanikai da ƴan kasuwan kan hanya na ‘Mechanic Village’ dake yankin Apo wajen aiki zuwa Wassa.

Sanarwar ta fito ne daga shugaban Majalisar, Felix Obuah a wata hira da manema labarai bayan ganawa da wikilan makanikan da na ƴan kasuwan da abin ya shafa, a ranar Talata.

Obuah, ya ce Wike ya tabbatar da aikin wanda aka shirya shi musamman don ƴan kasusuwar kan hanya da makamantansu kuma ya ce za’a fara korar su nan da wata ɗaya matuƙar basu tashi daga kasuwar ba.

Felix ya ƙara da cewa, tsawon shekaru 15 kenan ake ta ƙoƙarin sauya wa mutanen wajen harkokinnasu, saboda haifar da cinkoson ababan hawa da kuma kiyaye dokar hanyoyi a birnin Abuja, domin samun walwala a cikin al’umma.

Daga ƙarshe, ya ce za a bai wa waɗanda suka cike ƙa’idoji filaye a sabon wajen da aka sauya musu domin cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana.

By Babaji