Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda ya nemi haɗin kan al’ummar jihar Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Kebbi Bello M Sani kuma Kwamishina na talatin da bakwai da suka jagoranaci rundunar ‘yan sandan jihar ya nemi haɗin kan al’ummar jihar don samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Wannan bayanin yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Sufurtandan ‘yan sanda Nafi’u Abubakar da aka rabawa manema labarai ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Taƙara da cewa wannan jihar tana daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen zama lafiya daga cikin jihohin ƙasar nan.

Haka-zalika akwai alaqa mai kyau tsakanin al’ummar jihar tun kama daga ma’aikatan gwamnati zuwa ‘yan siyasa da kuma ‘yan kasuwa saboda haka yana da kyau wannan dangantaka ta ɗore a ci gaba da bai wa jami’an tsaro musamman ‘yan sanda haɗin kai ta hanyar kai rahotannnin duk wani abu da ba a gamsu da shi ba ko kuma waɗansu mutane a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Takardar ta bayyana cewa sabon kwamishinan ‘yan sandan wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar  Bakori ta jihar Katsina ne kuma yayen Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ne inda ya karancin Business Administration, kuma ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992 a matsayin Mataimakin Sufurtandan ‘yan sanda daga makarantar horon ‘yan sanda da ke Kaduna (Nigeria Police Academy, Anneɗ, Kaduna State.)

Kafin zuwansa a jihar Kebbi kwamishinan ‘Yan Sanda Bello M Sani ya yi ayyuka a wurare daban-daban da suka haɗa da sassa daban-daban, jihohi, yankuna da kuma babbar shalkwatar ‘yan sanda Abuja.

By ukarofi