Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan Majalisar Wakilai 50 sun aike wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu wasiƙar neman ya saki shugaban ƙungiyar ta’addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Honorabul Mohammed Jajere ya tabbatar wa Manhaja goyon bayansa ga buƙatar a saki Namadi Kanu, wanda ƙungiyarsa ta IPOB ke neman ɓallewa daga Nijeriya domin kafa ƙasar Biafra.
A halin yanzu dai Gwamnatin Tarayya tana gurfanar da shi a kan laifukan ta’addanci da kuma cin amanar ƙasa.
Mohammed Jajere ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu zai sa samu wanzajjen zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce wasiƙar da ’yan majalisar, ƙarƙashin ƙungiyarsu ta kishin Nijeriya ya ce, suka rubuta wa Tinubu ta “ba da shawarar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
“Shi ya sa muke roƙon Shugaba Tinubu ya amince a yi sulhu a wajen kotu domin a shawo kan lamarin.
“Ta wayar tarho aka sanar da ni abin da wasiƙar ta ƙunsa kuma na amince, don a samu zaman lafiya,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu ta wayar salula.
A wasiƙar da ’yan majalisar suka rubuta wa Tinubu ranar 19 Yuni 3024, sun buƙaci ya yi amfani da ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, ya umarci Ministan Shari’a ya janye ƙarar Nnamdi Kanu, a sasanta a wajen kotu.
Sun kuma ba da misali da cewa kafin yanzu Tinubu ya ba da damar yin irin wannan sulhu da Omoyele Sowore da kuma Sunday Adeyemi (Igboho) waɗanda su ma gwamnatin ta zarga da laifin cin amanar ƙasa.
Mambobin majalisar sun kuma buƙaci a samar da shirin samar da zaman lafiya domin tabbatar da aminci a yankin Kudu maso Gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.
Wasiƙar neman Tinubu ya saki Nnamdi Kanu
Wasiƙar da ’yan majalisar suka rubuta wa Tinubu ta ce: “Muna roƙon ka da ka umarci Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya yi amfani da ikon ofishinsa ya saki Nnamdi Kanu tare da janye ƙararsa a gaban kotu.
“Mun yi imanin cewa tun tuni ya kamata a yi hakan, wanda kuma zai buɗe ƙofar samun zaman lafiya, kawo cigaba tare da tafiya da kowane ɓangare.
“Hakan zai magance matsalar da ta haifar da kokensu, musamman ma idan aka yi gyara ga kundin tsarin mulki.
“Yin hakan zai kawo haɗin kan ƙasa tare da magance matsalolin tsaro da na siyasa da na tattalin arziki a yankin Kudu maso Gabas, wanda kuma zai bayu ga amincewar al’ummar yankin su shiga a tattauna da su kan al’amuran da suka shafi ƙasar nan.
“Sakin Nnamdi Kanu zai kawo karshen rikici da tsahin hankali a yankin sannan ya kawo wa yankin cigaba da bunƙasar tattalin arziki;
“Musamman a wannan lokaci da ƙasar nan take fama da matsalolin rashin ayyukan yi da na rashin tsaro da fatara da yunwa da rashin kwanciyar hankali.”
