Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘ya’yan babban attajirin nan na Jihar Legas, Marigayi Alhaji Ebetton a ƙarƙashin jagorancin ɗan uwansa Sarkin Musulmin Arab mazauna jihar Legas, Sultan Alhaji Jibirin Yaya ya jagoranci gudanar da taron addu’ar kwana bakwai da rasuwar ɗan uwansa Marigayi Alhaji Ebeto a Legas bakiɗaya.
Alhaji Ebeton ɗan shekaru tamanin da biyar ya rasu ne sanadiyyar gajeruwar rashin lafiya da ya yi a gidansa dake Maiduguri, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya ashirin da takwas a cikin ‘ya’yan nasa a kwai babban ɗansa Alhaji Muhammadu Gujja, jikoki da tattaɓa kunne da dama da fatan Allah ubangiji ya jiƙansa da rahama.
Taron addu’ar kwana bakwai da rasuwar marigayin ta samu halartar waɗansu daga cikin manyan malaman ƙasar nan da dama da sarakunan Hausawa na unguwanni daban-daban na jihar Legas da sarakunan Yarabawa da Nufawa da sarakunan sauran ƙabilu daban-daban na jihar Legas da sauran al’ummar Musulmi mazauna jihar Legas da kewayenta gaba ɗaya.
Taron ya gudana ne a harabar ƙofar gidan Marigayin Alhaji Ebetton dake Ƙiri-ƙiri Road Apapa cikin garin Legas.
Bayan buɗe taro da addu’a ne aka raba malaman masu gudanar da addu’o’in gida uku kashi na farko suka cigaba da karanto ayoyin alkƙur’ani mai tsarki kashi na biyu kuma suka cigaba da gudanar da addu’o’i tare da roƙon Allah Ubangiji ya jiƙan Alhaji Ebetton ya yi masa rahama yayin da kashi na uku suka duƙufa a wajen gudanar da addu’ọ’i na musamman domin neman amincewar Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya gaba ɗaya.
Kafin rasuwar marigayin Alhaji Ebeton yana riƙe da muƙamin sarautar Sardaunan Arab kuma Galadiman ‘yan Arewa mazauna jihar Legas. Sannan kuma uban ƙungiyar al’ummar Borno da Yobe a Legas da kewayenta gaba ɗaya.
Sarkin Musulmin Arab na jihar Legas Sultan Alhaji Jibirin Yaya ɗaya daga cikin ‘yan uwan marigayin Alhaji Ebetton a Legas ya bayyana cewar rasuwar marigayin rashi ne da ya girgiza dukkan al’ummar arewacin Nijeriya mazauna jihar legas da ma al’ummar Nijeriya baki ɗaya idan aka yi la’akari da irin gudummawar da yake bai wa ‘yan Arewacin Nijeriya mazauna jihar Legas.