An cafke wani kawali da ke kai wa ‘yan bindiga karuwai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani wanda yake kai wa ’yan bindiga karuwai domin yin lalata da su ya shiga hannun jami’an tsaro.

’Yan sanda sun bayyana cewa kawalin ya kuma ƙware wajen yin safarar makamai ga ƙungiyar jagoran ’yan bindiga mai suna Arɗo, wanda ake nema ruwa a jallo a yankin Kagarko da ke Jihar Kaduna.

An kuma gano cewa mutumin wanda yake harkar hada-hadar tura kuɗi ta PoS, shi ke kai wa iyalan ’yan bindiga kuɗaɗe a yankin na Kagarko.

Dubun kawalin ta cika ne a yayin wani samamen haɗin gwiwa da ’yan sanda suka gudanar a yankin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ya sanar ranar Talata cewa wanda ake zargin ya shaida musu cewa shi ke tsara yadda ake kai wa ’yan bindiga karuwai da miyagun ƙwayoyi da ma’aikatan lafiya a duk lokacin da suke buƙata.

“Ya kuma amsa cewa yana yin dakon kuɗi tare da rabawa ga iyalan ’yan bindiga.

“A cewarsa, kuɗaɗen da ya raba wa iyalan ’yan bindiga sun haura Naira miliyan ashirin,” in ji kwamishinan ’yan sandan.

Igwe ya ce wanda ake zargin ya tabbatar musu cewa ’yan bindigar da ke ƙarƙashin Ardo sun kai 15 kowannensu da bindiga ƙirar AK-47.

By ukarofi