Daga DAUDA USMAN a Legas
Wani babban dillalin sayar da doya a Legas kuma babban mai saukar baƙi masu kawo doya daga jihohin Nijeriya zuwa Legas, Alhaji Lado Yaro Jos ya bayyana yadda hauhawar farashin doya a samo asali a Legas.
Alhaji Lado Yaro Jos ya yi wannan tsokaci ne a Legas a lokacin da yake zantawa da wakilin Jaridar Blueprint Manhaja dangane da yanayin kasuwancin doya a Nijeriya da kuma matsatsin rayuwar al’umma bakiɗaya.
Alhaji Yaro, ɗan asalin Jihar Kano mazaunin Legas wanda yake gudanar da harkokin kasuwancin doya a kasuwar doya ta Shukura Yam Salas da ke kasuwar mile12, ya yi wannan bayani ne bisa ga yanayi da kuma dalilan da suka sanya doya da sauran kayan abincin da ake nomawa a Nijeriya ɗan karen tsada.
Ya ce, farashin abinci ya yi tashin gwauron zabi a kasuwan nin Nijeriya bakiɗaya.
Alhaji Lado Yaro Jos ya cigaba da bayyana cewa tashin farashin kayan abincin a kasuwannin Nijeriya ya samo asali ne tun gaba lokacin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayar da sanarwar janye tallafin take bai wa ɓangaren man fetur a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, harkokin kasuwanci na kowanne ɓangaren ya fara lalacewa a ƙasar nan ta huskar hauhawar farashin kaya a kasuwanni, wanda a cewarsa al’amarin da ya janyowa ‘yan Nijeriya matsalolin rayuwa daban-daban a ƙasar nan.
Lado yaro Jos ya cigaba da cewa, a wancan lokacin kafin Gwamnati ta bada shelar janye tallafin fetur a Nijeriya, ana shatar tirela mai ɗauko doya daga Okari ko Lafiya akan kuɗin da ba su wuce dubu ɗari huɗu da hamsin ba zuwa dubu ɗari biyar, kuma ba a biyan wani haraji akan hanya har shigowa Legas.
Ya ce, amma yanzu dalilin janye tallafin man fetur shatar tirela mai ɗauko doya daga garuruwan da suke nomarta zuwa Legas ya koma milyan biyu zuwa miliyan biyu da rabi. Sannan kuma ga biyan haraji a kowacce jiha kafin shigowa Legas.
Alhaji Lado ya ce, idan motar ta shigo Legas ɗin, direba da mai kaya sai sun yi fama da ’yan gareji a wajen ba su na-goro har zuwa inda za a sauke kayan.
Ta ƙara da cewa, kuma duk kuɗaɗen da aka kashe a hanya, za a sanya su ne a cikin kuɗin kaya, wanda halan zai sa dole kaya ya ƙara tsada a wajen mai saya.
Ya ce, akan haka yake roƙon Gwamnatin Jihar Legas da ta kawo wa ‘yan kasuwa da sauran masu shigowa da motoci Legas ɗauki dangane da wannan al’amari.
