Da ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta ɗage sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano zuwa jibi

Spread the love

A yayin da kotu ke cigaba da sauraren ƙarar rikicin masarautar Kano, yau babban kotun Jihar Kano ta ɗage sauraren ƙarar zuwa jibi, 4 ga watan Yuli.

Ƙarar da aka shigar 27 ga watan Mayu, tana neman sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da Sarkin Bichi, Gaya, Karaye da kuma Rano da su daina yawo suna kiran kansu sarakuna.

Waɗanda ake tuhuma, sun haɗa da Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Nasiru Ado Bayero, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da kuma Alhaji Ibrahim Gaya. Saura sun haɗa da sufeton ‘ƴan sanda, Darakta hukumar farin kaya, Sojoji da kuma Civil Defense.

Bayan sauraren duka ɓangarorin guda biyu, mai sharia Amina Adamu Aliyu,ta ɗage sauraren ƙarar zuwa jibi.

By ukarofi