Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A ƙarshen Babban Taron ƙungiyar Arewa Media Writers Association, da ta gudanar a garin Kaduna, an shawarci gwamnonin Arewa su kaucewa zubar da darajar sarautun gargajiya, saboda bambancin ra’ayin siyasa abin da ƙungiyar ke ganin rashin kishin Arewa ne ke haifar da haka.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin takardar jawabin bayan taron da ta yi da shugabannin ƙungiyar a matakin ƙasa da jihohi, ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban ƙungiyar na ƙasa Kwamred Haidar Hasheem Kano, inda ta fitar da wasu muhimman ƙudirori goma sha ɗaya.
Ƙungiyar ta yi kakkausan suka ga abin da ta ce, wasa da darajar sarakunan gargajiya, abin da ke neman zama abin yayi a tsakanin wasu gwamnonin ƙasar nan, musamman a nan yankin Arewa. Ƙungiyar ta nemi da a samar wa sarakuna matsayi na musamman a kundin tsarin mulkin ƙasa, da ba su ƙarfin ikon da zai ƙara ɗaga darajarsu a idon talakawansu da sauran ‘yan ƙasa. Ƙungiyar ta kuma bayyana takaicinta na yadda ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙaman gwamnati ke kawo ruɗani ga al’amarin masarautun gargajiya waɗanda su ne iyayen ƙasa da talakawa ke ganin darajarsu da kimarsu.
Kwamred Haidar Hasheem ya kuma ƙara da bayyana takaicin ƙungiyar Arewa Media Writers game da cigaba da ayyukan ‘yan bindiga a jihohin Zamfara, Sakkwato, Kaduna, Neja, da Katsina. Yayin da ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin rundunonin tsaro na ƙasa bisa ƙoƙarin da suke yi wajen samar da tsaro, tare da buƙatar a ƙara tsaurara matakan tsaro da samar da sabbin dabarun zamani na yaƙi da ayyukan ta’addanci da ‘yan tsagera.
Arewa Media Writers ta kuma la’anci alamun da ke nuna sake dawowar ayyukan ta’addanci na Boko Haram, inda ko a baya bayan nan an samu rahotannin da ke nuna cewa wani bam ya tashi a wani yankin Gwoza na Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu ‘yan Nijeriya. Bayan jajentawa al’umma da gwamnatin Jihar Borno bisa wannan mummunan al’amari, ƙungiyar ta nemi rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF ta tabbatar ba a bari tashin bama-bamai da amfani da ƙananan yara suna shiga ƙunar bakin wake, suna halaka rayuwarsu da ta sauran ‘yan Arewa, ya sake dawowa a sassan ƙasar nan.
Yayin da ƙungiyar ta jinjinawa ƙoƙarin da manema labarai ke yi wajen inganta tsarin dimukraɗiyya da wayar da kan ‘yan ƙasa game da haƙƙoƙinsu da ‘yancinsu, ta kuma buƙaci su cigaba da bankaɗo da muhimman batutuwan da suke damun al’ummar Arewa, don samar da mafita da shawarwari ga gwamnati da waɗanda abin ya shafa, domin ɗaukar matakan da suka dace.
Ƙungiyar ta kuma bayyana aniyarta na ɓullo da wasu hanyoyi na horar da ‘yan ƙungiya kan wasu muhimman ayyukan cigaban rayuwa da sana’o’in dogaro da kai, yayin da za ta cigaba da gogar da mambobinta a kan amfani da kafafen sadarwa na zamani, da yaƙi da rubuta labaran ƙarya.
Kwamred Haidar ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar ne, bayan da tsohon shugaban ƙungiyar na farko Kwamred Abba Sani Pantami ya ajiye shugabancin ƙungiyar bisa raɗin kansa.
An kafa ƙungiyar Arewa Media Writers ne a ranar 17 ga watan Yuli na 2020, da nufin haɗa kan matasa da ke rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta, da tsaftace irin rubuce-rubucen da ake yaɗawa marasa kyau, da kuma ƙarfafa marubuta bisa yaɗa batutuwan da suke fuskantar al’ummar Arewa, da yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.
