Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani jami’in hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna, Ya’u Inuwa, ya dawo da wayoyi biyu da suka ɓace waɗanda kuɗinsu ya kai Naira miliyan huɗu ga mai shi, Sheik Muhajjadina Kano a Jeddah.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Yunusa Abdullahi ne ya sanar da hakan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
Mista Abdullahi ya ce, “Malam Inuwa ya yi alfahari da jihar, a lokacin da ya miƙa wayoyin hannu guda biyu da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 4 ga mai shi a filin jirgin sama na Sarki Abdul Azeez a Jiddah, a lokacin da zai dawo Nijeriya.
An jiyo mai shi yana nuna godiya ga Malam Inuwa da ya mayar masa da wayoyin.
Ya ce ya manta da wayoyin ne a lokacin da yake jiran a tantance shi a filin jirgin.
Muhajjadina ya ce ya ajiye wayoyin ne a kan kujerarsa, yana tunanin suna cikin aljihunsa ne, sai a lokacin da za a duba shi, ya ƙara da cewa ya firgita lokacin da ya gano cewa babu wayoyin.
A cewarsa, wayoyin hannun na ɗauke da muhimman takardu da bayanai kuma suna da, wayoyin ƙirar iPhone 5 da iphone 15 Promaɗ.
“Jami’an tsaro na filin jirgin sun hana mu sauka daga benen da muka zauna a baya, don gano ko har yanzu wayoyin suna nan. Sun dage cewa da zarar an tantance fasinjoji, ba za su iya barin wurin da ake shiga ba.
“Muna cikin ruɗani a kan abin da za mu yi, sai wani jami’in Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna, ya tuntuɓe mu, ya bayyana mana cewa ya gano wayoyin da muka zauna a baya kafin a kira mu a tantance,” inji shi.
“Sheikh, wanda jami’in aikin Hajji ne na Jihar Kano, ya ce ya ji daɗi lokacin da aka dawo masa da wayoyin, kamar yadda ya yi addu’ar Allah ya saka wa Malam Inuwa bisa wannan aikin alheri da ya yi.
Mista Abdullahi ya ce Malam Inuwa shi ne jami’in rijistar Alhazai na ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna kuma ko’odinetan Jeddah na dawowar alhazai.
Ya ce baya ga wayoyin biyu, ya kuma mayar da jakunkuna bakwai na sauran fasinjojin.
Da yake magana kan yadda ya samu mai gidan, Mista Inuwa ya ce ya ga gungun jama’a suna kokawa kan asarar wayoyin hannu da aka yi a unguwar da aka kwana a filin jirgin.
Inuwa ya ce abin da ya yi ya yi daidai da aikinsa na aikin Hajji, inda ya ce alhazai su riƙa lura da kayansu musamman fasfo a filin jirgin
