Gwamnatin Tarayya ta kira taron gaggawa don warware batun zanga-zangar matsin rayuwa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jami’an Gwamnatin Tarayya sun shirya taron gaggawa don warware batutuwan shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba a Abuja, inda ya jaddada cewa gwamnati ba ta yin sakaci da ayyukanta tare da neman ƙarin lokaci daga ‘yan Nujeriya.

Idris ya ba da tabbacin cewa za a warware dukkan batutuwan domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar.

Ya ƙara da cewa, a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke martaba ‘yancin ‘yan ƙasa na gudanar da zanga-zangar lumana, gwamnatin ta ƙudiri aniyar hakan bai take haƙƙin sauran ‘yan ƙasa ba.

Mohammed Idris ya ce, suna da bayanan da ke nuna cewa wasu ɓata-gari na da niyyar fakewa da zanga-zangar wajen tayar da fitina.

“Shugaban ƙasa ba shi adawa da zanga-zanga, kawai dai yana ƙin tashin hankali da kuma duk wani abu da zai tauye walwalar ‘yan Nijeriya,” inji shi.

A wata ‘yar gajeriyar hirar da aka yi da shi bayan ganawar sirri, Idris ya bayyana cewa, “Mun taru ne domin tattaunawa. Kuna iya ganin hakan ba ya faruwa a zauren Majalisar. Yana faruwa ne a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma yawancin ministocin suna nan. Mun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya kuma dukkanmu muna yi wa Nijeriya aiki ne. Muna fata kuma mun yi imanin cewa Nijeriya za ta sake zama mai inganci.”

Da aka tambaye shi game da yadda gwamnati ke shiga tsakani da masu ruwa da tsaki da kuma masu shirya zanga-zangar, Mohammed Idris ya tabbatar da cewa ana ci gaba da warware batutuwan zanga-zangar.

By ukarofi