An farfaɗo da shari’ar mutanen da ake zargi da ta’addanci

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta ce ta ci gaba da shari’ar wasu mutane sama da 300 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci da kuma waɗanda ake zargi da aikata munanan laifuka a Nijeriya.

Wata sanarwa da shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) Abu Michael, ya fitar ta bayyana cewa, shari’ar ta biyo bayan ƙudirinta na inganta adalcin zamantakewar al’umma ta hanyar kafa tsarin gudanarwa na gaskiya.

Ya ce, shari’ar da ake ci gaba da yi wadda ta yi daidai da tsarin shari’ar manyan laifuffuka ta duniya, babbar kotun tarayya ta Nujeriya tare da Compleɗ Casework Group (CCG) na ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ne ke gudanar da shari’ar tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki a ƙarƙashinta.

A cewarsa, sama da mutane 300 ne ake tuhumarsu tare da manyan alƙalai 5 da ke kula da kotuna 5 da aka kafa domin gudanar da adalci cikin gaggawa kan shari’ar da ake yi na ta’addanci da sauran batutuwan da suka shafi ƙasar.

Ya bayyana cewa shari’ar ta haɗa da masu ruwa da tsaki da dama, da masu gabatar da ƙara na CCG, da kuma lauyan kare waɗanda ake ƙara daga ƙungiyar Legal Aid Council of Nigeria (LACON).

“Kafin yanzu, an sake duba fayilolin shari’o’i sama da 800, kuma an tsara tuhume-tuhume don ingantacciyar tuhuma don tabbatar da cewa an yi adalci.

“Tsakanin 2017 da 2018, gwajin ya zuwa yanzu ya haifar da hukunci 163, sallamar 882 da kuma wasu 5 da aka gurfanar. “Waɗanda ake zargin da ba su da laifi an sake su, suna gudanar da harkokin a gari,” inji shi.

Ya ƙara da cewa NCTC-ONSA tana aiki tuƙuru tare da hukumomin da abin ya shafa wajen cika ayyukanta da kuma bunƙasa ƙoƙarin gwamnati mai ci wajen tabbatar da shugabanci nagari da al’umma mai adalci. 

By ukarofi