Mu guji zanga-zanga a faɗin ƙasar nan – APC reshen Jihar Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) reshen Jihar Zamfara ta gargaɗi ‘yan jihar da su guji shiga zanga-zangar da a ke shirin yi a faɗin ƙasar saboda akwai yiwuwar haifar da hargitsi.

Shugaban jam’iyyar na jihar Hon. Tukur Umar Danfulani ya yi wannan gargaɗin a Gusau ranar Asabar.

Hon Danfulani ya bayyana cewa kiran ya zama wajibi saboda matsalar tsaro da ta addabi Zamfara da sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita kamar, Katsina, Kaduna, Sokoto da kuma Kebbi a Arewa maso Yamma, inda ya jaddada cewa akwai buƙatar zaman lafiyar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.

“Akwai yiyuwar ɓata garin matasa cikin zanga-zangar, don haka mu yi tunani mai kyau don guje wa ɓarnar da za’a yiwa ƙasarmu da sunan zanga-zanga saboda galibin ƙasashen da suka gudanar da irin wannan zanga-zangar a baya, yanzu suna fuskantar matsaloli fiye da abin da ya jawo zanga-zangar”. Yace

“Kamar a Sudan, al’ummar ƙasar sun yi zanga-zangar neman ragin farashin biredi amma a yanzu suna siyan biredi kan farashin da ya ninka sau biyar kafin farashin zanga-zangar da ɗimbin kadarorin ‘yan ƙasar, kayayyakin gwamnati, wuraren sana’o’i, wuraren kiwon lafiya, duk sun lalace inda mutane da dama suka rasa matsuguni. Kuma suka koma ‘yan gudun hijira a cikin ƙasarsu da makwabtanta”.

“Hakane a Libya, Siriya, da kuma na yanzu a Kenya don haka mu warware ƙorafe-ƙorafenmu ta hanyar tattaunawa domin babu wata ƙasa da za ta ci gaba ta hanyar zanga-zangar da za ta haifar da rikici.”

“Duk da cewa zanga-zangar nuni ce ta ‘yancin ‘yan ƙasa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su, amma duk hanyoyin da za a bi wajen magance matsalar cikin ruwan sanyi ba za a iya cewa sun ƙare ba.” Yace

A cewarsa Musulunci ya ƙyamaci zanga-zanga, kuma saboda tsoron irin ɓarnar da irin wannan zanga-zanga za ta iya haifar wa, yana da kyau a nemo wasu hanyoyin sasantawa.

Hon Danfulani ya bayyana shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu jagora ne mai saurare wanda yake yin iya ƙoƙarinsa wajen ganin Nijeriya ta zama wuri mai kyau ga kowa.

“Shugaba Tinubu ne kaɗai shugaban kasa da ya kai gwamnonin Nijeriya a gaban kotun ƙoli domin tabbatar da cewa gwamnati a matakin ƙasa ta yi cikakken aiki, wanda na yi imanin cewa ƙananan hukumomi sun samu cikakken ‘yancin cin gashin kai, matsalar rashin aikin yi, rashin tsaro, wahalhalu da sauran miyagun laifuka za su koma. tarihi a kasar”. Ya ƙara da cewa

Don haka mu ba shi goyon baya ta hanyar kyautatawa da addu’o’in da za su amfanar da zuriyarmu a gaba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa kada maƙiya ƙasar nan su tunzura matasa da suke ƙasashen waje suna jin daɗi da iyalansu kuma ba za su iya zuwa kusa da wuraren da ake gudanar da zanga-zangar ba sai dai kallo da sharhi a kafafen sada zumunta.

By ukarofi