Sanatar da ke wakiltar birnin tarayya ta musanta zargin da ake mata na ɗaukar nauyin zanga-zanga.
Idan ba mu manta ba, Blueprint ta rawaito ministan babban birnin tarayya ya na zargin cewa sanatar ta na ɗaukar nauyin zanga-zanga duk da bai fito fili ya kama suna ba.
Sai dai a wani martani da Sanata Kingibe ta fitar ta faifan bidiyo, ta yi tir da Allah wadai da wannan zargin, inda tace abokan hamayyar ta na siyasa ke yaɗa wannan ƙaryar domin a ɓata mata suna.
Kuma tace, ba za ta zauna ta ninke hannu yayin da ake ɓata mata suna ba, tabbas za ta ɗauki matakin da ya dace.
