
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ribar da aka samu a ɓangarorin tattali da zuba hannun jari a ayyuka su suka sa babu buƙatar yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.
A yayin wata ɗauka ta kai-tsaye, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta samu jimillar kuɗin shiga da adadinsu ya kai kimanin Dala tiriliyan 9.1 a kashin farko cikin biyu na shekarar 2024.
Ya ce gwamnatin tarayya ta rage bashi zuwa kashi 68 daga kashi 97 a shekarar 2023 cikin watanni 13. Sannan kuma ta samar da hanyar warware bashi a cinikayyar ƙasashen waje na Dala biliyan 5 ba tare da hakan ya yi tasiri wa cigaban ƙasar ba.
Tinubu ya ce ” watanni 14 da su ka gabata, gwamnatinmu ta sake gina tsare-tsaren haɓaka tattalin arziƙi da za su samar mana da gobe mai kyau.”
Shugaba Tinubu ya ce ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi ya sa jihohi da ƙananan hukumomi su ke karɓar kasafi mafi tsoka don inganta rayuwar al’umma a ɓangarorin ilimi da kiwon lafiya.
Haka nan, masana’antar mai da gas ta samu durƙushewa a baya wanda a yanzu ta farfaɗo, domin an samu ƙarin ganga miliyan 1.61 a man da ake samarwa a kowace rana, sakamakon haka masu hannun-jari su ka fara dawowa don cigaba da hulɗar kasuwanci a ɓangaren.
Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta nuna ƙoƙari da ta ke yi waje inganta rayuwar matasa ta hanyar samar da tsarin bayar da bashi ga ɗalibai wanda an ware Naira biliyan 45.6 da ke gaf da kai wa garesu inda ya yi kira ga matasa da su yi amfani da damar shiga tsarin don su samu gajiyarsa.
Gwamnatin ta kuma samu Dala miliyan 620 a ɓangaren kasuwancin zamani na komfuta (IDiCE) don inganta matasa da kuma samar da miliyoyin ayyukan yi ta yanar gizo domin gogayya da ƙasashen duniya.
Bugu da ƙari, sama da Naira biliyan 570 ne aka bai wa jihohi 36 don su bai wa al’ummarsu tallafi yayin da aka bai wa masu ƙananun sana’o’i su 600,000 tallafi. Sannan, wasu 400,000 za su amfana da tallafin a nan gaba.
