Zanga-zanga: Soyinka ya soki jawabin Tinubu

Spread the love

Farfesa Wole Soyinka ya soki jawabin shugaba Tinubu saboda a ciki bai yi Allah wadai da abinda jami’an tsaro suke yi ma masu zanga-zanga ba.

Soyinka ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar safiyar Lahadi, in da yace, jawabin ko kaɗan bai yi magana a kan irin hare-hare da jami’an tsaro ke kaiwa masu zanga-zangar lumana ba.

Soyinka ya bayyana cewa, yanayin matsi na rayuwa da yunwa a ƙasa shi ya sanya mutane suka fito don nuna fushin su. Amma abun kunya sai a ka samu jami’an tsaro suna harbin masu zanga-zangar nan don kawai sun fito sun nuna ɓacin rai a kan abunda ya kamata gwamnati ta yi wani abu a kai.

Ya cigaba da cewa, ya kamata jami’an tsaron ƙasar nan suyi koyi da takwarorinsu na ƙasashen ketare yadda su ke yi idan ana zanga-zanga ba wai harbin masu zanga-zanga ba.

Daga ƙarshe yayi kira da gwamnati tai gaggawar samar da mafita mai ɗorewa a kan batutuwa da masu zanga-zangar ke so.

By ukarofi