’Yan sanda sun tabbatar da kashe shahararren ɗan siyasa a Bauchi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani soja ya bindige wani fitaccen ɗan siyasa mai suna Habibu Aminu Dankasa a ranar Laraba a ƙauyen Lere da ke ƙaramar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi.

Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Wakili, lamarin ya ta’azzara ne bayan wata hatsaniya da ta ɓarke tsakanin ’ya’yan jam’iyyar PDP daga ƙauyen Lere da jami’an tawagar ‘Operation Safe Haɓen’ da ke Tafawa Balewa.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP daga ƙauyen Lere da ke aaramar hukumar Tafawa Balewa sun yi tattaki a cikin motocin Sharon guda uku domin gudanar da yaƙin neman zaɓe a gundumar Lere, gabanin zaɓen aananan hukumomin da ke tafe. Yayin da suke dawowa, jami’an ‘Operation Safe Haɓen’ sun tare su a wani shingen bincike, suka ƙi tsayawa suka wuce garin Lere.

Daga bisani sojojin sun kama ɗaya daga cikin direbobin a gidansa da ke Lere. Wannan matakin ya ƙara tunzura ‘yan ƙungiyar, lamarin da ya sa suka koma shingen bincike domin neman kuɓutar da direban da aka kama. Daga nan ne sojojin suka buɗe wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar Habibu ɗanƙasa tare da jikkata wasu da dama.

Wakili ya bayyana cewa, ’yan sandan sun mayar da martani ne bayan samun labarin.

“Kwamishanan ‘yan sanda, CP Auwal Muhammad, ya aike da rundunar ‘yan sandan wayar tafi da gidanka zuwa yankin domin ƙarfafa musu gwiwa.

Bugu da ƙari, an kafa wata tawagar kwararrun jami’an bincike da za su gudanar da cikakken bincike, kwararru da kuma bincike kan lokaci domin tabbatar da an yi adalci,” inji shi.

By ukarofi