Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Nijeriya, NUPRC, a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ce an samu rahoton wata gobara a rijiyar mai na Akaso gida huɗu da ke ƙarƙashin Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC).
Shugaban sashen hulɗa da jama’a na NUPRC, Laide Shonola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, 3 ga watan Agusta, 2024.
A cewar sanarwar, lamarin wanda ya tsawaita a gefen kogin an ruwaito cewa ya faru ne a ranar 2 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 11:12 na safe.
“NNPC 18 Operating Limited ta tabbatar da cewa an tura tawagar gaggawa don tabbatar da kashe gogara a rijiyar mai, da magance matsalar tare da ware yankin da abin ya shafa ta hanyar amfani da kayayyakin da ke ɗauke matakan kariya don hana ci gaba da gurbacewar muhalli.
“Suna kuma shirin fara aikin farfaɗo da man nan take. Kamfanin ya tura jirgin ruwan sojan ruwa a yankin da lamarin ya faru tare da kafa sa ido kan al’umma don sanya ido kan lamarin,” inji sanarwar.
Ya bayyana cewa har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.
A halin da ake ciki, hukumar ta ce ana shirin gudanar da bincike na haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki domin gano musabbabin da kuma yankin da abin ya shafa.
