NCC ta ba da umurnin rage farashin kira da data

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta umurci kamfanonin sadarwa da su duba tare da rage tsare-tsarensu na farashin kiran waya da na data.

A baya-bayan nan, da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun nuna ɓacin ransu game da yadda katin waya da data ke saurin ƙarewa ga kuma ɗan ƙaren tsada ba kamar a da ba.

Kakakin Hukumar NCC, Reuben Muoka, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya ce hukumar ta umurci dukkan kamfanonin sadarwa da su fitar da sahihin bayani, masu sauƙin fahimta game da farashin kira, tura saƙon SMS da kuma data ga duk masu amfani da layukan su.

Muoka ya ce hukumar ta miƙa wannan umarni ga kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, da sauransu a ranar 29 ga Yuli, 2024.

By ukarofi